Duk mai jayayya yazo na kai shi inda zai ci abincin 30 ya ci ya yi kat! – Nanono

Duk mai jayayya yazo na kai shi inda zai ci abincin 30 ya ci ya yi kat! – Nanono

Ministan harkokin noma a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Alhaji Sabo Nanono ya kara tabbatar da cewa akwai inda ake sayar da abincin N30 a koshi a jahar Kano, kuma duk mai jayayya da hakan yazo zai kaishi wajen.

Jaridar Kano Focus ta ruwaito a makon data gabata ne dai Nanono ya fara furta wannan magana, inda yace babu yunwa a Najeriya, wannan maganan ta janyo cecekuce a tsakanin yan Najeriya, musamman a shafukan sadarwar zamani.

KU KARANTA: Lambar yabo: Shugaban jami’ar ABU ya kere sa’anninsa a duk fadin Najeriya

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Nanono ya bayyana haka ne a ranar Litinin data gabata yayin bikin zagayowar ranar abinci ta duniya a babban birnin tarayya Abuja, inda yace: “Ina ganin muna samar da isashshen abinci, kuma ina tunanin babu yunwa a Najeriya, amma idan kunce akwai takura ba zan yi musu ba.

“Idan na ji mutane na maganan yunwa, sai dai kawai na yi dariya saboda na san basu san yunwa ba, idan da zaka je wasu kasashen, a nan ne zaka san me ake nufi a yunwa. Misali a Kano, zaka iya cin abincin N30 kuma ka koshi, don haka mu gode ma Allah saboda muna iya ciyar da kanmu, kuma abinci na arha a kasarmu.” Inji shi.

Sai dai a dalilin cece kucen da wannan magana ta sha, Ministan yace bai kamata yan Najeriya su yi ta zuzuta batun yunwa a kasar nan ba, inda yace yunwa itace idan mutum ya share kwanaki 10 ba tare da ya ci abinci ba.

“Zan iya zuwa Kano na kaika inda zaka samu abincin N30 ka ci ka koshi, mutane basu san me ake nufi da yunwa ba, amma sai su dinga kira ma kansu bala’i da sunan yunwa.” Kamar yadda ya bayyana a cikin hira da gidan rediyon Freedom.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng