Bayanai kan abinda Buhari da Osinbajo suka mallaka sirri ne - CCB

Bayanai kan abinda Buhari da Osinbajo suka mallaka sirri ne - CCB

Hukumar da ke binciken kadarorin ma'aikatan Najeriya CCB ta ce ba za ta iya bayyana bayyanan da ke kunshe cikin takardan bayyana kadarori na Shugaba Muhammadu Buhari, mataimakinsa Yemi Osinbajo da wasu tsaffin ma'aikatan gwamnati domin abinda ke ciki sirri ne da ba za a iya fadawa duniya ba.

Hukumar ta ce dokokin kasa a halin yanzu ba su ba ta ikon bayyana irin wannan bayanan ba sai dai idan Majalisar Tarayya ta yi wa dokar garambawul don a halin yanzu dai ba ta da ikon fadin abinda takardun suka kunsa.

CCB ta tana da takardan bayyana kadarori na shugabanin kasa, mataimakansu, shugabannin majalisa, gwamnoni da mataimakansu tun daga 1999 zuwa yanzu amma dukkan shugabanin sun ki bayar da izinin a sanar da al'umma abubuwan da ke cikin takardun da ya kunshe kadarorinsu.

DUBA WANNAN: 'Yan asalin jihar Filato sun cacaki Gwamna Lalong saboda ya nada bahaushe mukami

Hukumar ta yi wannan bayanan ne yayin bayar da amsa kan wata takarda da aka shigar a kotu na neman a bayyana abubuwan da ke cikin takardan kadarorin da Buhari da Osinbajo suka mallaka.

Wata kungiyar yaki da rashawa, wayar da kan al'umma da kwato hakokin al'umma da ake kira SERAP ne ta gabatar wa kotun tarayya da ke Lagos kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Wata babban ma'aikaciya a CCB, Ellis Adebayo wace ta bayar da amsa kan karar da SERAP ta shigar ta ce lauyan hukumar, Musa Ibrahim ya sanar da ita cewa doka ba bayar da ikon a sanar da SERAP bayyanan da ke cikin takardan kadarorin Buhari da Osinbajo ba.

Adebayo ta ce, "Takardun kadarorin shugaban kasa da ministocin Najeriya da ake neman suna dauke da bayannai na sirri kan kadarorinsu, abubuwan da suka mallaka da basusukansu da na 'ya'yan su 'yan kasa da shekaru 18 da matansu.

CCB ta ce babu wata doka da ta tilasta mata mika bayyanan ga kowa; kuma dokar Freedom of Information Act da SERAP tayi amfani da shi wurin shigar da bukatarta "ya ci karo da kundin tsarin mulkin kasa ta 1999 saboda haka ba zai yi aiki ba a nan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel