Kwamishinan Bauchi ya yi murabus bayan an sauya masa ma’aikata

Kwamishinan Bauchi ya yi murabus bayan an sauya masa ma’aikata

Kwamishinan kudi na jihar Bauchi, Alhaji Nura Manu Soro yayi murabus daga mukaminsa jim kadan bayan an mayar da shi ma’aikatar Matasa da wasanni.

Kwamishinan Labarai da Sadarwa na jihar, Ladan Salihu ya bayyana cewa gwamnan jihar Sanata Bala Muhammad ya yi sauye-sauye a majalisar sa.

Salihu ya bayyaa cewa gwamnan ya amince da canja ma Nura Manu Soro wajen aiki daga ma’aikatar kudi zuwa ma’aikatar matasa da wasanni; Umar Adamu daga ma’aikatar ruwa zuwa ma’aikatar kudi; Barrista Jadauna Tula daga ma’aikatar hada gwiwa zuwa ma’aikatar ruwa.

Sannan Usman Muhammed Saleh daga ma’aikatar matasa da wasanni zuwa ma’aikatar kananan sana’o’i.

Manu Soro wanda ya bayyana murabus dinsa ta shafinsa na facebook, ya yada cewa “Na yi murabus daga mukamina na kwamishinan kudi kuma mamba a majalisar zartarwa na jihar Bauchi. Zan gabatar da jawabai akan lamarin da yardar Allah."

An rantsar da Manu Soro tare da sauran kwamishinoni a ranar 11 ga watan Satumba. Ba a samu nasara ba wajen tuntuban Manu Soro don jin ra’ayinsa kan lamarin.

KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta mika godiya ga mijinta akan nada mata sabbin hadimai

Da aka tuntube shi, Babban hadimin Gwamna, Mukhtar Gidado ya bayyana cewa gwamnatin jihar bata karbi wasikar murabus daga Manu Soro ba a wannan lokacin, amman Manu Soro ya yada batun murabus din a shafinsa na twitter da facebook.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel