Abin mamaki: Dan damfara ya sayarwa da wani bature buhun gishiri naira miliyan 27 a matsayin buhun Lu'u-lu'u

Abin mamaki: Dan damfara ya sayarwa da wani bature buhun gishiri naira miliyan 27 a matsayin buhun Lu'u-lu'u

- Wai ance abin mamaki baya karewa, wani labari da muke samu ya bayyana cewa 'yan damfara da gaske suke a wannan shekarar

- A wannan lokacin sun kokarin barin tarihin da har yanzu ba a taba bari ba a duniya

- Kwanakin baya aka kama wani dan damfara da ya sayarwa da wani mutumi buhun gishiri a matsayin buhun Lu'ulu'u

Kwanakin baya an samu wani dan damfara da ya sayarwa da wani mutumi buhun gishiri akan kudi masu yawan gaske.

Baturen dai yayi tunanin wannan buhu na gishiri buhu ne na Lu'u-lu-u, sai ya bukaci ya sayi rabi, inda ya turo masa makudan kudade kimanin naira miliyan ashirin da bakwai, a matsayin idan sun gama ciniki zai sayi sauran, sai dai kuma baturen ya samu bugun zuciya bayan ya gano cewa wannan abu da ya siya buhun gishiri ne ba na lu'u-lu'u ba.

KU KARANTA: Lewis Latimer: Bakar fatar da ya fara kirkiro fitilar kwai da wayar tarho

Har ya zuwa yanzu dai an nemi wannan dan damfara sama da kasa an rasa shi a cikin kasar ta Ghana. Yanzu tambayar a nan ita ce shin wannan dan damfara yana son ya bata sunan kasar Ghana ne ko kuwa yaya?

A yayin da ake ta fama da matsalar 'yan damfara a Najeriya haka can ma a kasar Ghana ake fama da su kullum tamkar ba za su kare ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel