Lewis Latimer: Bakar fatar da ya fara kirkiro fitilar kwai da wayar tarho

Lewis Latimer: Bakar fatar da ya fara kirkiro fitilar kwai da wayar tarho

- Ba kowa ne ya damu da sanin mutane irin su Lewis Latimer duk kuwa da irin kokarin da yayi wajen kawo canji a duniyar da muke ciki

- Lewis shine mutumin da ya fara kirkiro wayar tarho da kuma fitilar kwai a karni na ashirin

- Lewis Latimer mutum ne bakar fata dan nahiyar Afrika, kuma shine ya kawo canji a bangaren fasaha da har yanzu ake mora a duniya

A wannan lokacin da muke ciki malamai ba su damu da koyar da dalibai tarihin bakaken fata irin su Lewis ba. Lewis Latimer har yanzu tarihin sa yana nan a rubuce a duniya, a matsayin dan Afrika da ya bar muhimmin tarihi a zamanin karni karni na 20. Shi ne mutumin da ya kirkiro wayar tarho, da kuma fitilar kwai.

An haifi Lewsi a shekarar 1848, inda iyayen shi wadanda suke bayi ne suka gudu daga hannun turawan wancan lokacin suka koma Boston da zama.

Lewis yayi aikin sojan ruwa a lokacin mulkin shugaban kasar Amurka Lincoln, a lokacin da yake da shekara 17 ya dawo garin Boston. Yana da basira matuka a bangaren zane-zane, bayan dawowarsa Boston da zama wani kamfani mai suna Crosby sun dauke shi aiki, inda yayi aiki da su na tsawon shekara 11.

Lewis ya fara kirkiro abu na farko a rayuwarsa a ranar 10 ga watan Fabrairun shekarar 1874. A lokacin ya kirkiri makwararar ruwa ne ta hanyar jirgi. A shekarar 1876 ya zana yadda wayar tarho take, ma'ana dai a lokacin bakin mutum yayi abinda ya canja duniya wanda har yanzu ake cin moriyarsa. Daga nan Maxim Hiram, wanda ya fara kirkiro bindiga mai linzami ya dauke shi aiki.

KU KARANTA: Duk jarumar fim da Daraktoci ba sa nemanta da lalata to ta binciki kanta, akwai matsala a tare da ita - Jaruma Vicky

Daga baya Lewis Latimer ya koma aiki da kamfanin Edison a matsayin injiniya, a lokacin shekarar 1879 fitilr kwai ana amfani da ita da itace ne, da takarda da sauran abubuwa inda take kaiwa tsawon sa'o'i 30 ba ta mutu ba.

A lokacin Lewis ya san akwai sauran aiki a gaban shi. A shekarar 1881, Lewis da abokinshi Joseph U. Nichols sun kirkiro fitilar kwai wacce take da inganci fiye da wacce suke amfani da ita a baya.

Lewis Latimer ya rasu a shekarar 1928 bayan yayi fama da matsananciyar jinya. Har yanzu ana girmama wannan mutumi bakar fata a matsayoin mutumin da ya kawo canji a karni na 20.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel