Illar da Fatima Mamman Daura ta yi ga nagartar shugaban kasa Muhammadu Buhari- Samuel Ajayi

Illar da Fatima Mamman Daura ta yi ga nagartar shugaban kasa Muhammadu Buhari- Samuel Ajayi

- A cikin kwanakin nan da aka dinga rade-radin karin auren shugaban kasa ne wani bidiyo ya dinga yawo wanda ke nuna an rufewa matar shugaban kasa kofa

- Amma kuma sai 'yar Mamman Daura ta fito ta bayyana gaskiyar lamari akan wannan bidiyon inda har take fadin shekarunsu uku a fadar shugaban kasa lokacin da aka dau bidiyon

- Amma kash, maganganun Fatima sun dasa kokwanto akan nagartar shugaban kasar da magoya bayansa ke ikirari

Wannan rubutu ra'ayin Samuel Ajayi ne kamar yadda aka wallafa a jaridar The Nation. Ba ra'ayin jaridar Legit.ng bane.

Idan da Fatima mamman Daura ta san illar da tayi ga nagartar Buhari, da bata baza bifdiyon nan ba ko kuma Magana da manema labarai.

Ga abinda ta ce: “Sunana Fatima Mamman Daura… Idan mutum ya yi tunani, zai gane cewa babu yadda za a yi a hana matar shugabaan kasa shiga wani sashi na gidan gwamnati. Sashin da aka Magana akai ana kiransa da ‘Glass House’. Kunsan akwai sassa da yawa acikin gidan gwamnati,”

Lokacin da shugaban kasa ya hau mulki, ya ba mahaifinmu Glass house ya zauna . Kunsan aminai ne kuma ‘yan uwan juna ne. Mun zauna a nan har tsawon shekaru uku zuwa lokacin da Yusuf ya samu rauni bayan ya dawo daga jinya daga kasar Jamus aka bukaci mu koma wani gida don yayi jinya a nan.”

KU KARANTA: Sabon salo: 'Yan sanda sun bukaci wata budurwa da ta nuna rasit din siyan karenta

Abu daya da magoya bayan shugaban kasar ke bayyanawa akan shugaban shine nagartarsa; ta yadda ba zai bar wata Baraka ta samu ba ko almubazzaranci a gwamnatinsa.

Amma kuma shi da kansa ya bawa dan uwansa sashi a fadar shugaban kasa.

Ba na gizo ke sakar ba, gaskiyar lamarin shi ne: Iyalan Mamman Daura na zaune a gidan ne tare da dogara akan gwamnati.

Idan mutum na rayuwa a gidan gwamnati, gwamnatin c eke daukar dawianiyar komai naka.

Daga kan ci da sha da sauran bukatun rayuwa duk gwamnati ce zata dau nauyinsu.

Motar da mutum ke hawa, ko ta gidan gwamnati ce, ko ta kansa, duk gwamnati zata dinga bashi man.

Wanki, ababen karrama bakinka da sauran bukatun rayuwa duk ya rataya a wuyan gwamnati.

A takaice dai Mamman daura da iyalansa sunyi rayuwar shekaru uku kenan suna morar gwamnatin Najeriya.

Tabbas, ta tabbata kuwa Buhari ya toshe barna da almubazzaranci.

Idan da ace Fatima Mamman Daura ta san wadannan tunane-tunanen da zasu shiga zukatan ‘yan Najeriya, da tabbas bata yi tereren nan ba.

https://www.solacebase.com/2019/10/16/mamman-dauras-daughter-and-the-dent-on-buharis-integrity/

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel