Arba'een: Za mu yi tattaki cikin Najeriya a ranar Asabar - IMN

Arba'een: Za mu yi tattaki cikin Najeriya a ranar Asabar - IMN

Mambobin kungiyar IMN wadda aka fi sani da Shi'a a Najeriya, sun bayyana aniyyarsu ta gudanar da tattakin nan na Arba'een a ranar Asabar wanda suka saba a kowace shekara.

Kamar dai sauran takwarorinsu na duniya, mabiya shi'a a Najeriya za su yi tattakin Arbaeen wato tuna wa da kisan jikan Manzon Tsira, Imam Hussain, a shekar ta 61 bayan hijira.

Kungiyar Shi'a na kuma gudanar da tattakin na Arbaeen dangane da ikirarin yadda aka daure wasu daga cikin 'yan uwan Manzo da sarka kuma aka rinka jansu a kar tun da ga garin Karbala na kasar Iraqi har zuwa Damashka na Syria.

Sai dai kungiyar ta tabbatar wa da al'ummar kasar nan cewa, za ta gudanar da tattakin nata cikin lumana da kwanciyar hankali ba tare da cuzguni ko kuma dakile hakkin kowane bil Adama ta kowace siga.

A rahoton da jaridar The Nation ta ruwaito, kungiyar yayin shan alwashi ta bayar da tabbaci, ta yi kira ga dukkanin al'ummar kasar a kan kada su tayar da hankulansu domin kuwa tattakin na Arbaeen ba zai kawo wata tangarda ba.

Furucin kungiyar ya zo ne a ranar Alhamis cikin wata sanarwa da kakakinta na kasa, Ibrahim Musa, ya gabatar. Ya ce akwai yiwuwar hukumomin tsaron kasar nan su kai musu hari yayin tattakin kamar yadda ta kasance a bara.

KARANTA KUMA: Abubuwa 10 da suka sha gaban Messi a yanzu

Ana iya tuna cewa, a watan Nuwamban shekarar 2017 ne kungiyar mabiya shi'a a Najeriya ta ce jami'an tsaron kasar sun kashe akalla mambobinta hudu, yayin da 'yan sanda suka tarwatsa wani tattaki da 'yan kungiyar suka yi a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel