Cakwakiya: Wani mutum ya auri surukarsa a matsayin mata ta biyu

Cakwakiya: Wani mutum ya auri surukarsa a matsayin mata ta biyu

Wani mutum dan kasar Malawi ya yi abin mamaki. Ya auri surukarsa a matsayin mata ta biyu bayan sunyi soyayyar a boue ta tsawon shekaru bakwai.

Kamar yadda rahoton ya nuna, mutumin mai suna Vashko Sande ya tsunduma soyayya da surukarsa shekaru kadan bayan aurensa da matarsa.

Tuni ya canza tare da fara cin zarafin matar tasa bayan da ya tsunduma a soyayya, har ta kai ga manyansa sun kasa dakatar da shi, lamarin da har ta kai ga ya tsallake al’ada ta hanyar auren surukar tasa.

Matar tasa, Vimbai Magora, ta kasa jure cin zarafin da mijinta ke mata har ta kai ga neman taimakon shari’a don bi mata hakkinta.

Mun yi aure a 2008 amma a 2011 mijina ya canza don ya fada soyayya da mahaifiyata. Ya fara dukana da zagina tare da barazanar korata da yarana hudu.” In ji Magora.

Ta cigaba da bayyana cewa, ko manyansa sun kasa shawo kan matsalarsu saboda baya jin shawara. Ya kuma cigaba da soyayya da surukarsa tare da watangarar da aurensa.

A yayin maida martani, Sande ya amsa zargin da ake masa inda ya bayyana cewa shi fa duk su biyun yake so kuma yana da burin kare rayuwarsa tare da su.

Da gaske ne ina kaunar surukata amma kuma inason matata. A don haka ne nake da burin kare rayuwata tare da su biyu,” a cewar Sande.

Kotun majistare ta bada umarnin zaman lafiya kamar yadda uwargidan ta bukata inda ta umarci Sande da kada ya kara cin zarafin uwargidansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel