Karin albashi: Zan biya ma'aikatan jiha ta fiye da N30,000 - Zababben gwamnan APC

Karin albashi: Zan biya ma'aikatan jiha ta fiye da N30,000 - Zababben gwamnan APC

Sabon zababben gwamna jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take ta biya ma'aikatan jihar Legas fiye da N30,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Da yake fadin hakan a ranar Talata, Sanwo-Olu, ya ce gwamnatinsa za ta fara biyan ma'aikata sabon karin albashi da zarar kungiyar kwadago (NLC) da gwamnatin tarayya sun cimma daidaito.

A cewarsa, gwamnatin jihar Legas na duba zurfin aljihunta tare da kirkirar sabbin hanyoyin shigowar kudi domin ta samu sukunin biyan ma'aikata karin albashin da aka yi.

Gwamnan ya furta wadannan kalamai ne yayin gana wa da shugabannin kungiyar kwadago a fadar gwamnatinsa da ke Alausa.

DUBA WANNAN: Boko Haram: An binne sojojin Najeriya 847 a iya makabartar sojoji ta Maiduguri - Sanata Ndume

Sanwo-Olu ya ce gwamnatinsa na sane da irin kalubalen yau da gobe da ma'aikatan jihar ke fuskanta, lamarin da yace shine yasa gwamnatin jihar ta yanke shawarar biyan fiye da mafi karancin albashin da aka kara, watau N30,000.

Sanna ya kara da cewa yana fatan hakan zai kara wa ma'aikatan jihar karsashi wajen gudanar da aiyukansu na yau da kullum.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel