Gwamna Ganduje yayi magana akan yaran jihar Kano da aka samo a Anambra

Gwamna Ganduje yayi magana akan yaran jihar Kano da aka samo a Anambra

- Gwamna Abdullahi Umar ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin kwatarwa yaran jihar Kano da aka sace aka siyar dasu a Anambra hakkinsu

- Gwamnan ya ce, za a kafa kwamiti mai karfi da zai binciko tushen matsalar tare da hanyoyin gujewar aukuwar hakan nan gaba

- Ya yi kira ga iyayen yara da su dinga sanya idanu akan 'ya'yansau tare da musu adddu'ar kariya daga miyagun mutane

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi alkawarin ganin cewa anyi wa yara 9 na jihar da aka sace, aka siyar a jihar Anambra adalci.

Gwamnan ya yi alkawarin na a ranar Talata inda ya tabbatar da cewa duk wani matakin shari’a da za a dauka don ganin anyi adalci garesu zai yi.

Ya tabbatar da cewa, wadanda aka kama kuma kae zargin da hannunsu a mummunan lamarin bazasu tafi haka ba. Dole ne su fuskanci fushin hukuma.

KU KARANTA: Dalilin da yasa na dade a kasar waje - Aisha Buhari

Wannan na kunshe ne takardar da sakataren yada labarai na gwamnan jihar, Abba Anwar ya bawa jaridar Solacebase a ranar Talata.

“Garkuwa da mutane abin ashsha ne kuma mummunan al’amari ne. Abin bakin ciki shine shekrun wadanda alka yi garkuwar dasu. Gwamnatina, mutanen jihar Kano da duk wani mai hankali ko kungiyoyi dole su yi al-wadai da hakan,” in ji gwamnan.

Ya jaddada cewa, kare hakkin dan adam ba tare da duba shekaru, kabila , addini ko siyasa ba, ginshiki ne na kowacce gwamnati. A don haka ne “Babu wani aikin laifi da za a bari ya tafi ba tare da hukunci ba,” ya ja kunne.

Ya bayyan cewa, kwamiti mai zaman kansa zai kafa don gano tushen wannan matsalar tare da kawo karshenta.

“Zamu kirkiro kwamiti mai karfi da zai duba lamarin da idanun basira don gano tushen matsalar tarae da magance aukuwar irinta nan gaba. A don haka muke bukatar hadin kan jama’a da jami’an tsaro don mu samu zaman lafiya da tsaro mai dorewa a jihar Kano” cewar gwamnan.

Ya kara da jawo hankulan iyayen yar da su zama masu saka ido akan yaransu tare da musu addu’ar kariya daga miyagu mutane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel