A karshe dai Dangote yayi martani ga gajeren wadan da yake bayyanawa duniya cewa ya fishi kudi

A karshe dai Dangote yayi martani ga gajeren wadan da yake bayyanawa duniya cewa ya fishi kudi

- Hamshakin dan kasuwan nan kuma mutum na farko da yafi kowa kudi a nahiyar Afrika ya mayar da martani ga wani gajeren wada

- Dangote ya mayar da martani ga gajeren wadan ne bayan ya fito yana bayyanawa duniya cewa ya fishi kudi

- Wadan wanda yake dan kasar Ghana ya fito a wani bidiyo ya bayyana cewa yafi Dangote kudi ya kuma bayyana shirinsa na zuwa yayi magana da mai kudin duniya Bill Gates

Hamshakin dan kasuwan nan Najeriya kuma wanda ya fi kowa arziki a nahiyar Afrika wato Alhaji Aliko Dangote ya mayarwa da fitaccen gajeren wadan nan dan kasar Ghana da ake kira da Shatta Bandle, wanda ya bayyana cewa yafi Dangote arziki.

Dangoten ya mayar da martani ga wadan ne bayan anyi wata hira da shi, inda ya ce:

"Ba zanyi gasa da kowa akan kudi ba, duk wanda ya ce ya fini kudi ni ina ganin ba matsala bane a wurina.

"Ba na gasa da kowa akan dukiya.

KU KARANTA: Tirkashi: Daliba ta bayyana yadda hirarsu da wani Lakcara ta kaya wanda ya nemi yayi zina da ita

"Ina da iya arziki na kuma ina matukar farin ciki da abinda Allah ya arzurta ni da shi.

"Bani da wani abu da zan nunawa duniya da zai bayyana cewa ina da kudi.

"Duniya ta san dani ne saboda irin ayyukan da na ke yi na taimakon al'umma."

Gajeren wadan wanda ainahin sunansa shine Idrissu Firdau, yayi suna sosai a kafafen sadarwa bayan ya fitar da wani inda yake bayyana cewa yafi Alhaji Aliko Dangote kudi, sannan kuma ya bayyana kudurinsa na zuwa yayi magana da mutumin da yafi kowa kudi a duniya, wato Bill Gates, inda ya bayyana cewa akwai wata harkalla da za su hada tare da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel