Gwamnonin jahohin Inyamurai zasu goga gemu da gemu da Buhari kan wata babbar bukata

Gwamnonin jahohin Inyamurai zasu goga gemu da gemu da Buhari kan wata babbar bukata

Kungiyar gwamnonin yankin kudu maso gabashin Najeriya sun yanke shawarar yin gemu da gemu da shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan bukatar bude filin sauka da tashin jirage a jahar Enugu, inji rahoton Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnonin zasu nemi karin kulawa da walwalar al’ummarsu daga gwamnatin tarayya a yayin ganawar da suke sa ran yi da shugaba Muhammadu Buhari nan bada jimawa ba.

KU KARANTA: Tsige Maja Sirdin Sarki ta janyo cece kuce da nuna ma juna yatsa a fadar Sarkin Kano

A kwanakin baya ne dai Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika ya bayyana ma kwamitin majalisar wakilan Najeriya dake kula da sufurin jirgin sama cewa ana bukatar naira biliyan 10 don gudanar da gyare gyare a filin jirgin.

Sai dai shugaban kungiyar gwamnonin yankin, Gwamna David Umahi na jahar Ebonyi ya bayyana matakin da zasu dauka bayan ganawa da kungiyar Ohanaeze, shuwagabannin addini da kuma yan majalisar yankin.

“Za mu tuntubi shugaban kasa game da walwalar jama’anmu na yankin kudu maso gabashin kasar nan, haka zalika muna fargabar gwamnati za ta iya mantawa da aikin filin jirgin nan, don haka zamu tuna masa.” Inji shi.

Daga cikin gwamnonin da suka halarci zaman akwai gwamnan jahar Abia Okezie Ikpeazu, gwamnan jahar Enugu Ifeanyi Ugwuanyi, mataimakin gwamnan jahar Imo Gerald Irona, amma ba’a hangi gwamnan jahar Anambra, Willie Obiano ba.

Haka zalika shugaban kungiyar kabilar Ibo ta Ohanaeze, Nnia Nwodo da kuma Sanata Enyinaya Abaribe a matsayin wakilin yan majalisun yankin sun halarci taron.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel