'Yan sanda sun rufe wata cibiyar azabtar da mutane da aka gano mutum 300 a daure

'Yan sanda sun rufe wata cibiyar azabtar da mutane da aka gano mutum 300 a daure

A ranar Litinin ne rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta gano wata cibiyar da ake azabtar da mutane masu tabin hankali a garin Daura, mahaifar shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan sanda sun kai samame cibiyar ne bayan mutanen da aka tsare a gidan sun yi tawaye a kan cin zarafinsu da ake yawan yi.

Wani mutum mai suna Malam Bello Daura, mazaunin garin Daura, shine wanda ya mallaki cibiyar, kuma an gano cewa cibiyar tafi shekara 40 tana aiki.

An gano fiye da mutane 300 a daure a cikin wasu kananan daki na tabo a cikin gidan.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Katsina, Sanusi Buba, ya bayyana cewa jami'an 'yan sanda sun gano wasu dakuna guda shidda kowanne da mutum 40 a daure da sarka a ciki

Buba ya kara da cewa jami'an 'yan sanda sun samu wasu daga cikin mutanen a daure da sarkoki da ankwar hannu.

Ko a cikin watan da ya gabata sai da jami'an 'yan sanda a jihar Kaduna suka gano irin wannan gidan da ake azabtar da yara a unguwar Rigasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel