Ba mutunci: Yadda Aisha Buhari ta yi mana 'tatas' a fadar shugaban kasa - Diyar Mamman Daura

Ba mutunci: Yadda Aisha Buhari ta yi mana 'tatas' a fadar shugaban kasa - Diyar Mamman Daura

Fatima Daura, diyar Mamman Daura, na hannun damar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta zargi uwargidan shugaba Buhari, Aisha Buhari, da far musu a cikin fadar shugaban kasa, Villa, dake Abuja.

Da take magana a kan wani faifan bidiyon da Aisha ke masifa a cikinsa saboda an rufe mata kofar shiga dakinta, Fatima ta ce ta yi mamakin irin yadda matar shugaba kasa ta rufe ido take ta masifa.

Faifan bidiyo ya kewaya a dandalin sada zumunta a daidai lokacin da ake rade-radin cewa shugaba Buhari zai angonce da Sadiya Umaru Farouq, sabuwar ministar harkokin tallafi da walwalar 'yan kasa.

A wata hira da ta yi da sashen Hausa na BBC, Fatima ta ce ta nadi faifan bidiyon ne domin ya zamar mata hujja a kan cewa Aisha ta yi musu 'tatas' a cikin fadar shugaban kasa.

Lamarin ya faru ne a cikin shekarar 2017.

A cikin sautin muryar Fatima da Legit.ng ta saurara, Fatima ta bayyana wurin da Aisha ke masifar an rufe ba bangarenta bane a cikin fadar shugaban kasa.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun rufe wata cibiyar azabtar da mutane da aka gano mutum 300 a daure

Ta bayyana cewa shugaba Buhari ne ya bawa mahaifinta, Mamman Daura, wurin a matsayin gidan da ya mallaka masa ya zauna.

Fatima ta kara da cewa daga baya bayan Yusuf, babban dan shugaba Buhari, ya dawo daga kasar Jamus, inda aka duba lafiyarsa bayan ya yi hatsari a babur, sai shugaba Buhari ya canja wa Mamman Daura gida saboda za a ajiye Yusuf a gidan domin a cigaba da yin jinyarsa.

Diyar ta Mamman Daura ta kara da cewa an yanke shawarar ajiye Yusuf a wurin ne saboda kusancinsa da bangaren da Aisha ke zaune, kuma ta yi ruwan wannan fada ne a lokacin da iyalin Mamman Daura suke tattara kayansu domin koma wa sabon gidansu.

A cewar Fatima, Aisha har jifan kofa ta yi da kujera saboda idonta ya rufe, ran ta ya baci saboda an rufe kofar wani daki a gidan da a baya ba a taba ganin ta shiga ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel