Da duminsa: Hukumar Kwastam ta yi mai 'dungurungum' a kan shiga da fita da kowanne irin kaya daga Najeriya

Da duminsa: Hukumar Kwastam ta yi mai 'dungurungum' a kan shiga da fita da kowanne irin kaya daga Najeriya

Hukumar hana fasa kwauri ta kasa da aka fi kira da 'Kwastam' (NCS) ta ce ba za a kara fitar da wani kaya ko shigo wa da shi cikin Najeriya ta kan iyakokin kasa ba.

Shugaban hukumar kwastam na kasa, Hameed Ali, ne ya bayyana hakan ranar Litinin yayin wani taro da manema labarai a Abuja.

Ali ya ce a halin da ake ciki yanzu, babu wasu kaya da za a iya shigo wa da su Najeriya sai ta iyakokin cikin ruwa, inda za a bincikarsu kafin su shigo cikin kasa jama'a su fara amfani da su.

Ya ce yin hakan zai bawa jami'an tsaro damar caje duk wani kaya da za a shigo da shi cikin Najeriya.

"Mu na fatan cewa a karshen wanna aiki da muke yi, za mu samu hadin kan makwabtan kasashe a kan irin kayan da za a shigo mana da su cikin kasa.

"Amma a haln yanzu, duk wasu kaya, masu illa ko akasin haka, ba zasu shigo ko su fita daga Najeriya ba.

"Ya kamata na kore shakku a kan wanna batu, ba za a shigo da duk wasu kaya ba, saboda duk kayan da ake shigo wa da su ta iyakokin kasa za a iya shigo wa da su ta iyakokin ruwa.

"A saboda haka, mu na shawartar duk masu shigo da kaya da su yi amfani da iyakokin cikin ruwa domin shigo da kayansu. Akwai isashen tsaro a iyakokin mu na ruwa, hakan zai bamu damar caje duk wani kaya da aka shigo da shi, " a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng