Rufe boda: Mun kwace kayayyaki 7 da kudinsu ya kai biliyan N1.4 a cikin wata guda

Rufe boda: Mun kwace kayayyaki 7 da kudinsu ya kai biliyan N1.4 a cikin wata guda

Shugaban hukumar hana fasa kwauri ta kasa da aka fi kira da 'Kwastam' (NCS), Hameed Ali, ya ce jami'an hukumar kwastam tare da hadin gwuiwar sauran jami'an tsaro da ke suntiri a kan iyakokin Najeriya da aka rufe sun samu nasarar kwace wasu kaya da darajar kudinsu ta kai biliyan N1.4 tun bayan rufe iyakokin Najeriya na kasa.

Ali ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Abuja yayin taron da suka gudanar da manema labarai tare da takwaransa na hukumar hana shige da fice ta kasa, Mohammed Babandede

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa jami'an tsaron cikin gida na hadin gwuiwa sun fara gudanar da wani atisaye mai taken 'Exercise Swift Response' a kan iyakokin Najeriya a ranar 29 ga watan Agusta.

An kafa rundunar jami'an tsaron ne domin tabbatar da tsaro domin kare lardin kasa, musamman iyakokin kasa da na ruwa saboda dalilan tsaro.

Atisayen na karkashin kulawar ofishin mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro (ONSA) a sassan Najeriya hudu da suka hada da; arewa maso yamma, arewa ta tsakiya, kudu maso yamma da kudu maso kudu.

DUBA WANNAN: Wutar lantarki: Jonathan da Buhari sun kashe tiriliyan N1.164 a cikin shekaru 8

Hameed Ali ya bayyana cewa kayayyakin da aka kwace tun bayan fara atisayen sun hada da; buhun shinkafa 21,071, motoci 190, duro 891 na man fetur da jarka 2,665 na man girki.

Ya ce ragowar kayan sun hada da babura 133, jarka 70 na man fetur da buhu 131 na takin zamani (NPK).

Shugaban hukumar Kwastam din ya bayyana cewa wasu bata gari na amfani da takin zamani (NPK) wajen hada sinadarai masu fashe wa.

Ya bayyana cewa an kama mutane 317 da ake zargi da sumoga da kuma karin wasu mutane 146 da suka shigo Najeriya ba bisa ka'ida ba.

Kazalika, ya bayyana cewa rufe iyakokin Najeriya ya jawo bunkasar kudaden shigo wa da hukumar kwastam ke samu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel