Uzoho, Aribo, da jerin ‘Yan wasan da su ka ba marada kunya a karawa da Brazil

Uzoho, Aribo, da jerin ‘Yan wasan da su ka ba marada kunya a karawa da Brazil

Kasar Brazil da Najeriya sun yi wata gwabzawa inda aka tashi kunnen doki da ci 1-1. Bayan dawowa hutun rabin lokaci ne Cesemiro ne ya soke kwallon da Najeriya ta ci a minti na 35.

Legit.ng ta kawo maku jerin ‘yan kwallo biyar da su ka fi kowa kokari a tsakiyar babban filin wasan kasar Singapore da aka buga wannan wasa. An yi wasan ne a Ranar 13 ga Okotoban 2019.

1. Joe Aribo

Joe Aribo ya zurawa Najeriya kwallonsa na biyu a tarihi a wasan. Matashin da ke take leda a kasar Scotland ya yi kokari a wasan na jiya musamman ganin cewa shi ne ya jefawa Ederson kwallo a raga.

2. Francis Uzoho

Wadanda su ka kalli wannan wasa sun yabawa kokarin mai tsaron ragar Najeriya Uzoho. Babban ‘Dan wasan ya nana kwarewarsa a lokacin da ya takawa harin Gabriel Jesus da Roberto Firmino’s burki.

KU KARANTA: 'Dan wasa Neymar ya na ji ya na gani Brazil ta gaza doke Super Eagles

3. Chidozie Awaziem

‘Dan wasan bayan kungiyar CD Leganes, Awaziem ya rikide a wasan na Super Eagles da Gwarazan Amurka. Awaziem ya hana Firmino da Everton watayawa kamar yadda su ke so a wasan.

4. Wilfred Ndidi

‘Dan wasan tsakiyan Leicester City mai tare, Wilfred Ndidi, ya sake yin abin da ya saba. Ndidi ya yi kokari a tsakiyar fili duk da cewa yana tare da ‘dan wasan Real Madrid Casimero da kuma irinsu Arthur.

5. Samuel Chukwueze

Matashi Chukuwueze mai tashi a sama ya nunawa ‘Yan wasan Brazil irin baiwarsa. ‘Dan kwallon na Villareal ya rika yanke Yaran na Samba. Sai dai akwai bukatar ya dage wajen iya cin kwallo a wasansa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel