Barayin gwamnoni na bukatar babban shiriya daga Allah – Gwamnan Nasarawa

Barayin gwamnoni na bukatar babban shiriya daga Allah – Gwamnan Nasarawa

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, yace duk wani mutum da aka zaba a matsayin gwamnan wata jiha bai da hujjar satar kudin jama’a.

Sule ya bayyana hakan a lokacin rufe taron gasar Al-Qur’ani na kasa karo na 23 wanda kungiyar Izala ta shirya a Lafia, babbar birnin jihar Nasarawa.

A cewar gwamnan, duk wani mutum da aka zaba a matsayin gwamna sannan aka same shi da satar kudin jama’a toh yana bukatar shiriya daga Allah.

Sule ya bayyana cewa an tanadarwa da gwamnoni komai ta yadda shaidani ne kadai zai bige da sata.

“A lokacin da na karbi Shugabanci a matsayin Gwamna, sai na gane cewa wadanda basu da ilimin sanin Allah na iya sata ko kuma wadanda babban aikinsu shine satar kudaden jama’a."

Sule yayi amfani da damar wajen kira ga malamai da shugabanni masu ilimi da su shiga siyasa a matsayin wani hanyar kawo tsarki a tsarin.

KU KARANTA KUMA: Maraba da Ganduje: Sarki Sanusi ya tube rawanin wani babban basarake a fadarsa

Yayi watsi da hasashen cewa sai mutum ya zama mai arziki kafin ya shiga siyasa, inda ya kara da cewa idan har malaman addini zasu dunga gudun siyasa toh su shirya zabar shugabannin da za su ci amanar su.

Ya kuma yi kira ga malamai akan kada su gaji da fadama mutane gaskiya, koda ba za su ji ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel