Caseimero ya ceci Kasar Brazil a hannun ‘Yan Najeriya bayan an tashi 1-1

Caseimero ya ceci Kasar Brazil a hannun ‘Yan Najeriya bayan an tashi 1-1

Tawagar ‘Yan wasan Super Eagles na Najeriya sun tashi canjaras da kasar Brazlil inda aka yi kunnen doki. An buga wannan wasa ne a babban filin kwallon kafa na kasar Singapore dazu nan.

Ana take wasa ‘dan wasan gaban Najeriya Victor Osimhen da ke buga wasa a Lille ya nemi ya kai kwallo a ragar Brazil. Ederson Moraes mai tsaron gida ne ya yi kokarin hana kwallon shiga zare.

Najeriya ta cigaba da taka rawar gani a wasan kafin Gabriel Jesus ya kai wa mai tsaron ragar Super Eagles din watau Francis Uzoho wani hari da kai. Daga baya an cire Neymar Jr. a wasan.

Super Eagles sun samu nasara ne ta hannun Joe Aribo. ‘Dan wasan tsakiya Aribo mai taka leda a tsakiya ne ya kutsa bayan Yaran Samba inda ya sirdado kwallon da ta wuce Moraes a cikin raga.

KU KARANTA: 'Dan wasan PSG Neymar Jr. ya kafa tarihi a kasar Brazil

‘Yan wasan gaban Najeriya Victor Osimhen da Moses Simon su ne wadanda su ka yi rawar gani wajen kwallon da Najeriya ta ci a minti na 35. Haka aka tafi hutun rabin lokaci ana dukan Brazil.

Bayan an dawo hutu kenan ‘Dan wasan tsakiyan Real Madrid, Casemiro ya jefa kwallo a cikin ragar Super Eagles. Tun da Casemiro ya jefa wannan kwallo, babu wanda ya iya sake ganin raga.

Daga baya an canza Simon da Emmanuel Dennis inda aka kuma jefa Ramon Azeez a gurbin Alex Iwobi a gaba. S. Chukwueze da kuma J. Aribo sun ba Peter Olayinka and Abdullahi Shehu wuri.

Daga canjin da Brazil ta yi akwai inda Philippe Coutinho ya canji Tauraro Neymar Jr. Richarlison ya canji Everton yayin da Gabriel Barbosa, Fabinho da Lucas Paqueta su ka shigo daga baya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel