Shaidanun gwamnoni ne kadai za su saci dukiyar talakawansu - Abdullahi Sule

Shaidanun gwamnoni ne kadai za su saci dukiyar talakawansu - Abdullahi Sule

Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule, ya ce matukar wani gwamna ba ya da shaidaniyar zuciya, to kuwa babu abinda zai sa ya kai hannu kan dukiyar talakawansa.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, gwamna Sule ya bayyana hakan ne a yayin rufe taron musabakar Al-Qur'ani ta kasa karo na 23 wanda kungiyar Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa Ikamatus Sunnah ta gudanar a ranar Asabar cikin birnin Lafiyan Nasarawa.

Gwamna Sule ya bayyana cewa an tanadarwa gwamnoni dukkanin bukatarsu ta yadda shaidani ne kadai zai bige da satar dukiya daga baitul malin talakawansa.

A cewar gwamnan, duk wani mutum da aka zaba a matsayin gwamna sannan kuma aka same shi da satar kudin jama’a to kuwa babu shakka yana da bukatar shiriya daga Allah.

Sule yayi amfani da damar wajen kira ga malamai da shugabanni masu ilimi da su shiga siyasa a matsayin wata mafificiyar hanyar ta kawo tsarki a tsarin.

KARANTA KUMA: Rashin sa ido da iyaye ke yi ya sa tarbiyya ta lalace a jihar Kano - Sheikh Umar Fagge

Yayi watsi da ra'ayin cewa sai mutum ya zama mai arziki kafin ya shiga siyasa, inda ya jaddada cewa idan har malaman addini za su rinka gudun siyasa to kada su yi kuka idan shugabanni sun ci amanar su.

Ya kuma yi kira ga malamai akan kada su yi kasa a gwiwa wajen kiran mutane zuwa ga shiriya tare da fada masu gaskiya, koda kuwa za su yi watsi da ita.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel