Gwamnatin Zamfara ta gano sarakuna da jami'an tsaro masu hannu a matsalar tsaron jihar

Gwamnatin Zamfara ta gano sarakuna da jami'an tsaro masu hannu a matsalar tsaron jihar

Wani kwamitin gudanar da bincike a kan matsalar tsaro da jihar Zamfara ke ci gaba da fuskanta wanda gwamna Muhammadu Bello Matawalle ya kafa, ya gano wadanda ke da hannu kan haifar da wannan mummunar annoba a jihar.

Kwamitin ya gano cewa wasu bata garin jami'an tsaro na soji da kuma na 'yan sanda gami da sarakunan gargajiya na da hannu wajen assasa matsalar rashin tsaro a jihar.

Yayin mika rahoton a ranar Juma'ar da ta gabata, jagoran kwamitin binciken wanda ya kasance tsohon sufeto janar na 'yan sandan Najeriya, Alhaji M.D Abubakar, ya ce an gano cewa wasu sarakuna 5, dagatai da masu unguwanni fiye da 40 masu hannu cikin badakalar rashin tsaro a jihar.

Haka kuma binciken ya tattaro cewa akwai jami'an soji 10, da 'yan sanda gami da wasu ma'aikatan gwamnatin dake aiki tare da 'yan bindiga masu tayar da zaune tsaye a jihar Zamfara.

Kamar yadda Muryar Duniya ta ruwaito, binciken ya tabbatar da cewa a tsakanin watan Yunin 2011 zuwa watan Mayun 2019, 'yan bindiga sun karbi kudin fansa da ya haura naira biliyan 3 daga hannun mutane kimanin 3,600 da suka yi garkuwa da su a jihar.

Yayin ci gaba da hikaito irin asarar da matsalar tsaron ta haddasa a jihar, tsohon sufeton na 'yan sanda ya ce hare-haren 'yan bindiga a tsakanin shekaru kimanin takwas da suka shude kawo yanzu, ya yi sanadiyar jefa yara 25,000 cikin maraici tare da raba mutane kimanin 200,000 da muhallansu.

KARANTA KUMA: Matan jihar Adamawa sun nemi a haramta aurar da su a kananun shekaru

Hakazalika, Makiyaya sun yi asarar fiye da shanu 2,000, tumaki, awakai, jakuna da kuma rakuma da sun haura 2,500 a sanadiyar hare-haren 'yan daban daji. An kuma tafka asarar ababen hawa da suka hadar da motoci da babura fiye da 147,000 a tsawon shekaru 8 da bullar matsalar a jihar.

Tsohon babban jami'in tsaron na kasa ya kuma shawarci gwamnatin jihar Zamfara akan hanyoyi tumke damararta domin tabbatar da aminci na dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma a jihar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel