Yadda ruwa ya ci mutane 38 a jihar Bauchi

Yadda ruwa ya ci mutane 38 a jihar Bauchi

Har yanzu ana cigaba da juyayin mutuwar wasu mutane 38 a cikin wani ruwa da ke yankin karamar hukumar Kirfi a jihar Bauchi. Lamarin da ya faru ranar 7 ga watan Oktoba, 2019, ya bar mutane cikin alhini har yanzu.

Faruwar hatsarin ya nuna yadda matsalar rashin hanyoyi ke haifar da wahalar rayuwa ga mazauna yankin karkara.

Babu wata hanya da mutanen kauyukan Guyaba, Beni da Shongo ke sufuri da ta wuce ta hanyar amfani da kwale-kwale domin tsallaka kogin Gongola da ya rabu su da juna.

Masu bulaguro kan shafe kimanin sa'o'i biyar suna tafiya a cikin ruwa.

Mutanen da suka mutu a cikin kwale-kwalen da ya yi hatsarin sun fito ne daga kauyuka da dama da suka hada da; Kuna, Badara, Kesu, Beni, Shongo, Butta, Wuro, Chedi, Maigari da Baba Ladi.

Musa Isa, daya daga cikin wadanda suka rayu a cikin jirgin, ya ce yawan jama'ar da aka loda ne ya hadda hatsarin jirgin.

"Sai da na yi gargadin cewa mun yi yawa a cikin jirgin amma babu wanda ya saurare ni, dan uwana, Hassan, na daga cikin wadanda suka mutu a hatsarin jirgin," a cewarsa.

Wani manomi, Abdullahi Tsando, mazaunin garin Bara, ya ce jirgin, wanda ya taso daga kauyen Kesu, ya gamu da hatsarin ne bayan sitiyarin da ake sarrafa jirgin ya karye, lamarin da yasa injin ya tsaya cak a tsakiyar ruwa.

"Jama'ar cikin sun firgita duk da matukin jirgin ya yi kokarin kwantar musu hankali. An cikin jirgin jugum-jugum kawai sai wani mutum ya yi Allan-baku ya fada cikin ruwan. Nan da nan sai jama'a suka jirkita zuwa bangare daya na jirgin, lamarin da yasa ruwa ya fara shigowa ciki sakamakon nutsewar da ya fara yi.

"Ni ma tsalle na yi na fada cikin ruwan, amma a hakan wani ya rike min kayan jikina, sai da cizo na kwaci kai na," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel