Bidiyo: Iyayen wata budurwa sun shiga har aji sun ciccibo saurayin da ya dirkawa 'yarsu cikin shege

Bidiyo: Iyayen wata budurwa sun shiga har aji sun ciccibo saurayin da ya dirkawa 'yarsu cikin shege

- Wani lamari da ya faru a wata jami'a a kasar Ghana ya ba wa mutane da yawan gaske dariya da mamaki

- Yayin da iyayen wata yarinya da 'yan uwanta suka shiga ajin da ake koyar da karatu suka ciccibo saurayin yarinyar

- An bayyana cewa dai saurayin ya yiwa yarinyar cikin shege ne dalilin da ya sanya suka dauko shi domin bin ba'asi

Alamu na nuni da cewa yawaitar zinace-zinace na karuwa a makarantun kasar Ghana musamman ma jami'o'i da koda yaushe ake samun cudanya tsakanin maza da mata.

Wani lamari ya faru a wata jami'a dake kasar ta Ghana yayin da iyayen wata budurwa suka biyo saurayinta makarantar da yake suka shiga ajin da yake daukar karatu suka ciccibo shi suka fito dashi domin jin dalilin da yasa ya yiwa 'yar cikin shege.

Wasu wanda lamarin ya faru a kan idon su sun bayyana cewa wurin ya barke da hayaniya bayan iyayen yarinyar da 'yan uwanta sun shiga dakin karatun da saurayin yake, a yayin da dalibai masu tarin yawa suke daukar darasi a ajin.

KU KARANTA: Bidiyo: Allah ya tona asirin wasu mazinata, yayin da mazakutar namijin ta makale jikin macen bayan sun gama lalatar su

Wannan lamari dai yana zuwa ne bayan an tonawa wasu Malaman Jami'a guda biyu asiri da suke yin lalata da dalibai mata kafin su bari su haye jarrabawar su.

Wannan tonon silili dai wata wakiliyar BBC ce tayi wannan namijin kokari mai suna Kiki Mordi, wacce ta yi badda kama taje wata jami'a a matsayin dalibar dake neman gurbin karatu, inda shi kuma malamin ya nemi hadin kanta kafin ya bata gurbin zama a makarantar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng