Ga irinta nan ai: Yadda aka daure wani Sarki a jikin mota aka dinga jan shi layi-layi saboda yaki cika alkawuran da ya dauka kafin a zabe shi

Ga irinta nan ai: Yadda aka daure wani Sarki a jikin mota aka dinga jan shi layi-layi saboda yaki cika alkawuran da ya dauka kafin a zabe shi

- Wasu fusatattun mutane sun yiwa Mai garinsu dukan tsiya suka kuma daure shi a jikin mota suka yi ta jan shi a kasa

- Mutanen sun yiwa mutumin wannan hukunci ne bayan yayi musu wani alkawari kafin su zabe shi amma bayan ya hau kujera yaki cika musu

- Mai garin ya bayyana cewa zai kai kara kotu akan abinda mutanen garin suka yi masa na kokarin kashe shi

Wani shugaba (Sarki) ya ga ta kansa a wajen mutanen shi, bayan yayi kunnen uwar shegu yaki cika musu alkawuran da ya dauka lokacin da yake so ya hau kujerar mulkin garin.

Rahotanni sun bayyana cewa mutumin mai suna Jorge Luis Escandon Hernandez, shine shugaban garin Las Margaritas dake kasar Mexico, 'yan garin ne suka yi masa wannan aika-aika bayan yaki cika musu alkawuran da ya dauka a lokacin da yake yakin neman zabe, na cewa zai gyara musu hanyoyin cikin gari.

KU KARANTA: Dan sanda abokin kowa: Dan sanda ya yiwa wani mai mota dukan tsiya, saboda kawai yazo ya wuce shi a mota

Fusatattun mutanen sun fito da Mai garin ta karfin tsiya inda suka daure shi a jikin wata katuwar mota suka dinga jan shi a kasa kwararo-kwararo layi-layi na cikin garin na Las Margaritas.

Mai garin ya bayyana cewa zai kai kara kotu akan sace shi da aka yi, da kuma kokarin kashe shi da mutanen garin suka yi.

A yanzu haka dai an kama sama da mutane goma sha daya (11) domin fara bincike a kansu, kamar yadda Tabasco Al Minuto ta bayyana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel