Kwamishinan ‘yan sanda na son a sanya hukuncin kisa ga masu laifukan cin-hanci

Kwamishinan ‘yan sanda na son a sanya hukuncin kisa ga masu laifukan cin-hanci

Alhaji Ali Aji-Janga, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna a ranar Laraba yayi kira ga gwamnatin Najeriya na tayi kwaskwarima ga hukuncin masu laifin cin-hanci ta hanyar sanya daurin rai da rai da kuma kisa a ciki.

Kwamishinan ya fadi wannan maganar ne a yayin da ya halarci wani taro na musamman da aka gudanar a Zaria, inda aka tattauna yadda za iya shawo kan matsalar tsaron Najeriya.

KU KARANTA:Badakkalar naira miliyan 12: EFCC ta kama ma’ajin wata masarauta daga jihar arewa

Kamfanin dillacin Najeriya, NAN ta sanar damu cewa Ali-Janga shi ne babban bako na musamman a wurin taron da kwalejin kimiyya da kere-kere ta Nuhu Bamalli ta shirya.

Kwamishinan wanda ya samu wakilcin ACP Surajo Mohammed-Fana ya ce akwai bukatar an tsaurara hukunci ga masu aikata laifukan cin-hanci ganin yadda yake kawowa Najeriya rashin cigaba.

Ali-Janga ya ce: “Zai yi matukar kyawo idan akayi kwaskwarima ga hukuncin masu laifin cin-hanci da rashawa a Najeriya. Ta hanyar sanya daurin rai da rai da kuma kisan a matsayin hukuncin masu laifin.

“Mutanen da ake samu dumu-dumu da tarin dukiyar jama’a ba kawai karbe kudin za ayi ba, kamata yayi a hanasu sake rike wani mukamin gwamnati gaba daya rayuwarsu.

“Maganar dakile cin-hanci a kasar nan ya kamata a ce ya wuce matakin muhawara a kasar nan yanzu, sai dai a ce wajibine.” Inji Kwamishinan.

Kwamishinan ya kara da yin kira ga matasa a matsayinsu na manyan gobe da suke mike tsaye wurin yaki da cin-hanci a kasar nan, domin gyaran Najeriya.

https://tribuneonlineng.com/cp-advocates-death-penalty-for-corrupt-practices-in-nigeria/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel