Karin harajin kaya: Za a yi amfani da kudaden a fannin lafiya, ilimi da gine-gine – Buhari

Karin harajin kaya: Za a yi amfani da kudaden a fannin lafiya, ilimi da gine-gine – Buhari

Yayinda ya gabatar da kasafin kudin 2020 a majalisar dokokin tarayya a ranar Talata, 8 ga watan Oktoba, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da rabe-raben yadda za a kashe kudaden da aka samu daga Karin harajin kaya.

Da yake magana da yan majalisa a zauren majalisar dokoki da ke Abuja, Shugaba Buhari ya bayyana cewa kudaden da aka samu zai tafi ga jihohi da kananan hukumomi a kasar.

Ya kara da cewa za a yi amfani da kaso 85% na kudaden shigar wajen daukar nauyin fannin lafiya, ilimi, ababen more rayuwa a fadin kasar domin amfanin yan Najeriya.

Shugaba Buhari yace: “Yayinda za a tura kaso 85 na dukkanin kudaden da aka samu daga karin harajin kaya zuwa ga jihohi da kananan hukumomi, muna sanya ran ganin inganci sosai wajen kashe kudadensu a wadannan bangarori sosai."

KU KARANTA KUMA: Ma'aikatun gwamnatin tarayya da suka samu kaso mafi tsoka a kasafin kudin 2020

A wani lamarin kuma Legit.ng ta rahoto a baya cewa Hukumar da ke lura sha’anin wutar lantarki a Najeriya ta NERC ta rubutawa kamfanoni 8 da ke da alhakin raba wuta takarda inda ta yi barazanar karbe lasisinsu a dalilin bashin da ke wuyansu.

Bashin Naira biliyan 30.1 da ake bin wadannan kamfanonin wuta ne ya sa wani Kwamishinan NERC ya nemi su yi bayani mai gamsarwa cikin kwana 60 domin su ceci lasisin aikinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel