An ba hammata iska tsakanin wasu maza biyu da wani jami’i mai ba motoci hannu (bidiyo)

An ba hammata iska tsakanin wasu maza biyu da wani jami’i mai ba motoci hannu (bidiyo)

Masu iya magana sun ce idan da ranka ka sha kallo, a kullun abubuwan ban mamaki da al’ajabi na faruwa a tsakanin al’umma, ta yadda mutane kan ci mutuncin junansu a sarari ba tare da jin kunya ko la’akari da doka ba.

Hakan ne ya kasance a wani bidiyo da ya shahara a yanar gizo na wasu mutane da suka ba hammata iska tare da wani mai ba motoci hannu.

A cikin bidiyon an gano wasu magidanta biyu sun tarar ma jami’in dokar inda suka dunga dukansa.

Koda dai ba a bayyana lokaci ko wurin da abun ya faru ba, wani abokin aikin mai ba motoci hannu yayi nasarar raba fadan.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan APC ya tsige hadiminsa bayan ya yi wa Mai dakinsa izgili

A wani labari na daban, mun ji cewa Kotun Majistare da ke Kaduna a ranar Litinin ta bayar da umurnin tsare malaman islamiyyan Ahmad Bn Hambal da 'yan sanda suka kama a wani gidan gyaran tarbiya.

'Yan sandan sun kai sumame makarantar a ranar 27 ga watan Satumba a Rigasa Kaduna inda suke gano dalibai fiye da 300 da aka yi ikirarin cewa ana cin zarafinsu tare da keta hakkinsu.

Daily Trust ta ruwaito cewa nn gurfanar da malaman shida ne a gaban alkalin kotun, Musa Lawaal Mohammed na kotu ta 16.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel