Wata sabuwa: An fara yiwa 'yar jaridar BBC da ta bankado yadda Malamai ke lalata da dalibai a jami'a barazanar kisa

Wata sabuwa: An fara yiwa 'yar jaridar BBC da ta bankado yadda Malamai ke lalata da dalibai a jami'a barazanar kisa

- Wakiliyar BBC da taje ta bankado irin wainar da 'yan iskan malaman jami'a ke toyawa ta fara samun barazanar kisa

- 'Yar jaridar mai suna Kiki Mordi, ta bayyana cewa wasu daga cikin mutanen da wannan bincike na ta bai yi musu dadi ba sun fara yi mata barazanar kisa

- Sai dai ta ce wannan abu bai dame ta ba saboda ta san cewa BBC za ta dauki kwakkwaran mataki akan su

Kiki Mordi, 'yar jaridar BBC da tayi badda sawu domin ta tonawa malaman jami'a asiri akan abinda suke yi na lalata da dalibai kafin su basu maki, yanzu haka dai ta fara samun barazanar kisa daga wajen mutanen da wannan tonon silili bai yi musu dadi ba.

Kiki wacce tace ita kanta ta shiga wannan hali, inda malami ya bukaci yayi lalata da ita a lokacin da take jami'a.

Ta bayyana cewa ta fara samun barazana akan wannan bincike da ta yi, inda aka bayyana ta da kuma wasu 'yan uwanta 'yan jarida mata a lokacin da suke daukar bidiyon wasu malaman jami'a na Legas da kuma wasu a kasar Ghana a boye, inda malaman suke amfani da mukamin da suke dashi suna lalata da dalibai mata kafin su basu maki.

Sai dai ta ce ita bata damu da wannan barazana da ake yi mata ba, saboda ta san cewa BBC tana karfafa tsaro ga dukkan ma'aikacin da suka dauka aiki.

KU KARANTA: Iskancin jami'a ba a kan maza ya tsaya kawai ba, Malamai mata ma suna bukatar dalibai suyi lalata da su kafin su basu maki - 'Yar jarida

"Naji dadi matuka na ganin irin sauyin da ake samu tun a lokacin da aka saki bidiyon, kuma ina tabbatar muku da cewa daya daga cikin malaman jami'ar Legas din an kama shi dumu-dumu yana neman yayi lalata da wata daliba da taje neman gurbin karatu a jami'ar, yanzu haka ma an kore shi daga jami'ar.

"Ina fatan cewa abin ba zai tsaya a nan ba kawai har sai an samu canji yadda ya kamata a kasashen mu na Afrika."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel