Babbar magana: Masu garkuwa da mutane sun sace 'yan sanda a Ribas

Babbar magana: Masu garkuwa da mutane sun sace 'yan sanda a Ribas

Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace jami'an 'yan sanda guda biyu a garin Ngor, hedikwatar karamar hukumar Andoni a jihar Ribas.

Dukkan jami'an 'yan sandan na aiki ne tare da hedikwatar rundunar 'yan sandan jihar Ribas, kuma an sace su ne ranar Litinin.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ribas, DSP Nnamdi Omoni, ya tabbatar da faruwar lamarin. Sai dai, har yaznu rundunar 'yan sandan jihar Ribas ba ta bayyana sunayen jami'anta da 'yan bindigar suka sace ba.

DSP Omoni ya yi alkawarin fitar da jawabi a hukumance, nan bada dade wa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel