Sulaiman Adamu: Ministan Buhari ya ce jiharsa ta fi kowacce jiha kazanta a arewa

Sulaiman Adamu: Ministan Buhari ya ce jiharsa ta fi kowacce jiha kazanta a arewa

Ministan albarkatun ruwa, Suleiman Adamu, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Jigawa ta gaza a bangaren tsaftar muhalli biyo bayan kasancewarta mafi koma baya a yankin arewa maso yamma a alkaluman tsaftar muhalli da aka fitar.

Ministan ya bayyana hakan ne ranar Talata, lokacin da ya ziyarci gwamnan jihar Jigawa, Muhammed Badaru Abubakar, a Dutse, babban jihar Jigawa.

Ya ce lamarin bai kamata ya cigaba da tafiya a haka ba tare da yin kira ga gwamna Badaru da ya saka dokar ta baci a bangaren tsaftar muhalli a jihar Jigawa.

Adamu ya jinjina wa gwamnatin jihar Jigawa bisa samun nasara da kaso 86.8 a bangaren samar da ruwan sha mai tsafta ga mutanenta.

"Duk da kasancewar ni dan asalin jihar Jigawa ne, dole mu fada wa kan mu gaskiya cewa jihar Jigawa ta gaza a bangaren tsaftar muhalli. Hakan ne yasa ta zama mafi koma baya a yankin arewa da ma kasa baki daya.

DUBA WANNAN: Wadume: Kwamiti ya bayyana sunan soja da jami'an 'yan sanda 4 da ya kamata a ladabtar

"Duk da jihar Jigawa ta samu nasara da kaso 86.6 a bangaren samar da ruwan sha mai tsafta ga jama'a, amma akwai bukatar inganta tsaftar muhalli," a cewar Adamu.

Da yake mayar da martani ga jawabin Ministan, gwamna Badaru ya amince cewa akwai kalubale ta fuskar tsaftar muhalli a jiharsa tare da bayyana saka dokar ta baci a bangaren kamar yadda ministan ya bukata.

"Za mu ke gudanar da taro kowanne sati domin magance matsalar rashin tsaftar muhalli a jihar Jigawa. Za mu aika kudirin neman haramta yin bahaya a fili zuwa majalisar jihar domin ta yi doka a kai," a cewar gwamna Badaru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel