An tsige mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Taraba

An tsige mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Taraba

Mambobin majalisar dokokin jihar Taraba sun tsige Honarabul Mohammed Gwampo, mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar.

Jaidar The Nation ta ruwaito cewa an tsige Gwampo ne a zauren majalisar a ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba.

Gwampo ya kasance dan majalisa mai wakiltan mazabar Yorro a majalisar dokokin na jihar Taraba.

Legit.ng ta rahoto a baya cewa an harrgitsa zaman majalisar dokokin jihar Bayelsa bayan wasu yan daba sun kai mamaya harabar majalisar.

KU KARANTA KUMA: Tsirarun mutane da ke zaune a jihohi 5 ne suka tattare arzikin Najeriya - Buhari

An kuma tattaro cewa yan daban na ta harbi ba kakkautawa a sama inda hakan ya sanya yan majalisa da saura mutanen da ke harabar majalisar tserewa.

A wani labari na daban kuma mun ji cewa an karfafa tsaro a ciki da wajen kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Bauchi yayinda Alkalan kotun ke zaman raba gardama tsakanin gwamnan jihar, Bala Mohammad na jam'iyyar PDP da Mohammed Abubakar na jam'iyyar APC.

Jami'an tsaro wadansa suka hada da yan sanda, jami'an NSCDC, jami'an DSS da wasu na leken asiri sun mamaye titin Ahmadu Bello way da titin Yandoka da safiyar nan.

Punch ta ruwaito cewa an kulle hanyar gaba daya kuma an umurci mutane su bi wasu hanyoyin daban. Hakan ya kawo matsala ga masu motoci haya, yan kasuwa da ofishohin ma'aikatan gwamnati da aka kulle.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel