A makon da ya gabata an kashe sojoji 38 da fararen hula 16 a Najeriya

A makon da ya gabata an kashe sojoji 38 da fararen hula 16 a Najeriya

A makon da ya gabata cikin fadin Najeriya, rundunar dakarun ta tafka babbar asara, inda rayukan dakarun soji kimanin 38 suka salwanta a sanadiyar aukuwar munanan hare-hare kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Fararen hula 6 da 'yan daban daji 10 sun rasa rayukansu a yayin aukuwar wasu munanan hare-haren a fadin kasar nan inda kimanin mutane 16 suka afka tarkon masu ta'adar garkuwa da neman kudin fansa.

Daya daga cikin mafi munanan hare-haren ya auku ne a ranar Alhamis, inda aka kashe dakarun soji 9 a jihar Zamfara da kuma wasu 11 daban a jihar Borno. Haka kuma a wannan rana ce aka sace wasu dalibai mata shida da malamai biyu a wata makarantar jihar Kaduna.

Alkalumma sun tabbatar a cewa ya zuwa ya yanzu kungiyar masu tayar da kaya baya ta Boko Haram ta salwantar da rayukan fiye da mutane 30,000 a tsawon kimanin shekaru 10 da daura damarar ta'addanci a kasar nan musamman yankin Arewa maso Yamma da kuma wasu kasashen da ke makwabtaka da Najeriya.

Hakazalika, garkuwa da mutane tare da neman kudin fansa na daya daga cikin manyan hanyoyi da kungiyar ke ribata wajen tara dukiyar ci gaba da huro wutar yaki da zaman lafiya a kasar.

Wannan musiba ta sanya a ranar Litinin ta makon da ya gabata, shugaban hafsin sojin kasan najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya ce lamarin Boko Haram ya ci tura a kasar da dole a yanzu sai an dukufa wajen kwarara addu'o'i domin Mahallacin Sammai da Kassai ya jibinci lamarin.

KARANTA KUMA: Boko Haram: An bai wa malamai 30 kwangilar addu'a a Saudiyya

Ana iya tuna cewa, a ranar Lahadin makon da ya gabata ne rundunar dakarun sojin kasan Najeriya ta zargi wani babban soja da ya kai mukamin Manjo da kuma wasu sojoji 21 da laifin tsere wa daga filin daga, lamarin da ya sanya rayukan dakaru kimanin 18 suka salwanta a wani mummunan hari da ya auku cikin yankin Gubio na jihar Borno.

A wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridat Legit.ng ta ruwaito, hukumar 'yan sanda a jihar Taraba ta ce rayukan mutane 5 sun salwanta a sanadiyar arangamar da ta auku tsakanin 'yan kabilar Tibi da Jukun a karamar hukumar Donga ta jihar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel