Abin dariya a kotu, yayin da wanda ake tuhuma yabi alkali da itace zai rafke, bayan ya yanke mishi hukuncin da bai yi masa ba
- Wani bidiyo da yake ta faman yawo a kafar sadarwa ya bai wa mutane da dama dariya
- Lamarin dai ya faru tamkar wasan kwaikwayo ne yayin da wani mutumi da alkali ya yanke masa hukunci a kotu ya dauki katon sanda yabi alkalin zai rafke
- Bayan mutanen dake cikin kotun kowa yayi ta kansa ya gudu sai mutumin ya koma dukan kujeru da tebura dake cikin kotun
Wani abin dariya da ya faru a wata kotu dake kasar Zimbabwe ya sanya mutane dariya a kafar sadarwa, bayan da wani mutumi mai laifi ya bi alkalin kotun da itace zai rafke, bayan alkalin ya bayyana cewa yana da laifi akan abinda yayi aka kai shi kotun.
A wannan bidiyo mai abin dariya da yake ta yawo a shafukan sada zumunta na zamani, an hango mutumin wanda ya aikata laifin da katon itace yana korar duka mutanen dake cikin kotun.
KU KARANTA: Bayan aurena ya mutu sau biyu, mutane suna ta zargin cewa lalacewa zanyi - Laila Ali Othman
Inda mutane suka fara gudun nemawa kansu lafiya kada ya rafke su, da ya nemi kowa ya rasa a cikin kotun, sai ya koma dukan tebura da kujerun dake cikin kotun.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng