Kwamacala: Budurwa ta auri samari guda biyar rigis duka 'yan uwan juna a lokaci daya

Kwamacala: Budurwa ta auri samari guda biyar rigis duka 'yan uwan juna a lokaci daya

- A ka'ida dama kowa ya san cewa an halattawa namiji ya auri mace fiye da daya

- To amma kuma wani sabon al'amari da ba kowane ya saba jin shi ba shine yadda wata budurwa ta auri maza guda biyar rigis a lokaci daya

- Budurwar ta auri mazan ne wadanda suke 'yan gida daya ne duka su biyar din

Rajo ta fara aurenta da mijinta na farko mai suna Guddu Verma mai shekaru 23, a tsarin al'adarsu ta India, bayan shekara hudu sai ta auri sauran 'yan uwansa guda hudu, Baiju mai shekara 32, Sant Ram mai shekara 28, Gopal mai shekara 26 da kuma Dinesh mai shekara 19, wanda ya aureta a lokacin da ya cika shekara 18 a duniya.

Kwamacala: Budurwa ta auri samari guda biyar rigis duka 'yan uwan juna a lokaci daya
Rajo Family
Asali: Facebook

Rajo ta ce a farko dai taji wani iri, amma yanzu ba ta jin komai dan tana auren maza biyar. Ta kuma ce ba ta nuna banbanci a tsakaninsu. Ta na zaune da mazajen nata guda biyar a daki daya ne. Ita ce ke gyaran daki, ta dafa abinci ta kuma lura da 'ya'yansu, inda su kuma mazajen za su fita wajen aiki.

Dakin da suke zaune ko gado babu a ciki, kasan dakin kuma an saka bargo ne aka shinfida. Ta ware lokaci da take kwanciya da kowanne a cikinsu.

KU KARANTA: Jaruma Fati Washa ta sha tofin Allah tsine a wajen masoyanta bayan ta wallafa wani hotonta na tsiraici

Mijinta na farko Guddu ya bayyana cewa ba ya wani kishi dan 'yan uwan nasa suna auren matar tashi, ya kuma bayyana cewa yana jin dadin rayuwar da suke yi.

Kwamacala: Budurwa ta auri samari guda biyar rigis duka 'yan uwan juna a lokaci daya
Rajo Family
Asali: Facebook

Rajo ta bayyana cewa abin sun kamar gado ne saboda mahaifiyarta ita ma ta auri wasu samari ne 'yan gida daya guda uku a lokaci daya, inda ya zama al'adar kauyensu idan zaki yi aure ki auri duka 'yan gida daya a lokaci daya koda kuwa su nawa ne.

Ta kara da cewa tana samun kulawa da soyayya fiye da mata masu mazaje daya. Haka kuma tana da yaro mai watanni 18 a duniya, ta kuma bayyana cewa a cikin mazajen nata guda biyar ba za ta iya ware mahaifin yaron ba.

Ba wannan ne karo na farko da muka fara kawo muku irin wannan labarin ba, inda dazun nan muka kawo muku labarin yadda wata tsaleliyar budurwa ta auri kare a kasar ta Indiya.

Kwamacala: Budurwa ta auri samari guda biyar rigis duka 'yan uwan juna a lokaci daya
Rajo Family
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel