Allah mai iko: Wani Kirista da yake zuwa Masallacin Juma'a yana shiryawa masallata takalmansu sannan yayi musu gadi

Allah mai iko: Wani Kirista da yake zuwa Masallacin Juma'a yana shiryawa masallata takalmansu sannan yayi musu gadi

- Wani abin mamaki da ya faru a kasar Singapore ya bar mutane suna ta tofa albarkacin bakinsu akan wani mutumi Kirista mai suna Uncle Steven

- Mutumin dai yana da wata al'ada ta zuwa wani Masallacin Juma'a duk ranar Juma'a yana shiryawa mutane takalman su

- Mutumin ya bayyana cewa yana yin hakan ne saboda yana ganin shirya takalman yana da matukar amfani domin suna yin kyau idan aka shirya su

Wani Kirista wanda aka fi sani da 'Uncle Steven' ya dauki wata al'ada ta zuwa Masallacin Juma'a na Al-Mawaddah dake kasar Singapore yana shiryawa mutanen da suka je Sallah takalman su sannan kuma ya tsaya yayi musu gadi har a idar da sallah.

Wani mutumi mai suna Irfan Mustapha, shine ya wallafa hoton wannan mutumi a shafinsa na Facebbok. Mustapha ya ce yana ganin mutumin ranar kowacce Juma'a yana yin abu daya a Masallacin.

Allah mai iko: Wani Kirista da yake zuwa Masallacin Juma'a yana shiryawa masallata takalmansu sannan yayi musu gadi
Steven
Asali: Facebook

KU KARANTA: Tirkashi: 'Yan sanda a kasar Afrika ta Kudu sun yiwa 'yan kungiyar Biafra da suka fito yiwa shugaba Buhari ihu harbin Kan mai uwa da wabi

Da aka tambayi mutumin dalilin da ya sanya shi yake wannan abu, sai ya bayar da amsa mai sauki ya ce:

"Sun fi kyau idan aka shirya."

Ya ce yana kokarin zuwa kowacce Juma'a ne saboda gidan da yake bashi da nisa da Masallacin.

Mustapha ya ce ya jima yana mamakin kokari irin na wannan mutumi.

Allah mai iko: Wani Kirista da yake zuwa Masallacin Juma'a yana shiryawa masallata takalmansu sannan yayi musu gadi
Steven and Mustapha
Asali: Facebook

"Na jima ina lura da Uncle Steven, nayi matukar mamakin ganin irin kokarin da yake yi duk da cewa shi ba Musulmi bane," in ji Mustapha.

Wannan abin da Uncle Steven yake yi yayi matukar bai wa mutane da yawan gaske mamaki, inda wasu suke yi masa fatan Allah yasa hakan ita ce hanyar shiriyar sa ya dawo addinin Musulmi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel