Bidiyo: Yadda aka yiwa wasu 'yammata a makarantar sakandare bidiyo suna madigo a bainar jama'a

Bidiyo: Yadda aka yiwa wasu 'yammata a makarantar sakandare bidiyo suna madigo a bainar jama'a

- Wani bidiyo da yake ta faman yawo a kafar sadarwa ta zamani ya bayyana wasu 'yammata guda biyu suna rawar iskanci

- Bidiyon ya bayyana yadda 'yammatan wadanda suke dalibai ne suke rawar iskanci suna kama jikin junansu

- Wannan lamari dai ya faru a wata makarantar sakandare ne ta kasar Ghana, inda lamarin ya bar alamar tambaya da yawa a wajen mutane dangane da tarbiyar yara a wannan kasar

Wani bidiyo da yake ta yawo a kafafen sadarwa ya bayyana yadda wasu dalibai mata 'yan makarantar sakandare dake kasar Ghana suke iskanci da jikin junansu, ma'ana suke madigo.

An hango 'yammatan suna rawa suna kuma kama jikin junansu a lokacin da aka hada wani bikin holewa a makarantar, can daga baya kuma an nuno 'yammatan sun fara wuce gona a iri, inda aka bayyana su suna rike wuraren da bai kamata ba a jikunnan su.

KU KARANTA: A karon farko matar gwamna a wata jihar arewacin Najeriya za ta fito takarar gwamna

A yayin da suke aikata wannan masha'a kuwa dalibai 'yan uwansu suna gefe suna kallon ikon Allah, inda wasu daga cikin daliban suka fara yin amfani da wayoyinsu suna daukar su bidiyo.

Har yanzu hukumar ilimi ta kasar Ghana ba ta yi magana dangane da wannan dabi'a ta daliban ba na wannan abu da aka kama su suna yi, amma dai bidiyon ya riga ya yadu a kafar sadarwa, inda mutane da dama suka sanya alamar tambaya akan fannin ilimi na kasar.

Ga bidiyon yadda abin ya faru a kasa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng