A karon farko matar gwamna a wata jihar arewacin Najeriya za ta fito takarar gwamna

A karon farko matar gwamna a wata jihar arewacin Najeriya za ta fito takarar gwamna

- Matar marigayi tsohon gwamnan jihar Kogi Abubakar Audu ta sha alwashin fitowa neman kujerar gwamnan jihar a zaben da za ayi ranar 16 ga watan Nuwambar nan

- Aisha Abubakar Audu ta bayyana kudurinta na fitowa ne a jam'iyyar YPP

- Ta ce za ta fito domin ta karasa ayyukan alkhairi da mijinta ya fara bai kammala ba a jihar

Tsohuwar matar gwamnan jihar Kogi, Aisha Abubakar Audu ta fito da gasken-gaske domin damawa da ita wajen neman kujerar gwamnan jihar.

A cewar Aisha, idan aka zabe ta a ranar 16 ga watan Nuwambar nan, za ta kawo karshen talauci, cin hanci da rashawa da kuma sauran abubuwan da ba su kamata ba a fadin jihar.

A wata sanarwa da aka fita daga ofishin ta, wacce aka bayyanawa 'yan jarida a Abuja jiya Laraba, Aisha za ta fito takarar gwamnan ne a jam'iyyar Young Progressive Party (YPP).

Aisha dai ita ce matar da tsohon gwamnan jihar Kogi, Abubakar Audu ya mutu ya bari, kuma a cewarta ta yanke hukuncin fitowa takarar ne a jam'iyyar YPP, bayan shugabannin jam'iyyar sun bukaci da ta fito.

KU KARANTA: Tsugunne ba ta kare ba a jihar Kano: Mun daukaka kara a kotun Kaduna - Abba Gida-Gida

"Jam'iyyar YPP ta yi karfi sosai a 'yan watannin nan a jihar Kogi.

"Iyalan marigayi Abubakar Audu za su shigo cikin harkar siyasar jihar nan domin su karasa abubuwan da tsohon gwamnan ya rasu bai yi ba.

"Ta riga ta gama bin duk wata ka'ida ta hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, kuma an riga an bayyana sunanta a matsayin 'yar takara. Yanzu lokaci ne da ya kamata a shiga lungu da sako a sanar da mutane abubuwan alkhairin da za ta yi," yadda sanarwar ta bayyana kenan.

Aisha Abubakar 'yar asalin jihar Kogi tana daya daga cikin mata guda uku da suka fito neman takarar gwamnan jihar a ranar 16 ga watan Nuwamba, inda ta zabi Mr. Suleiman Ozigi a matsayin abokin takarar ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel