Maganar tazarcen da Buhari yake yi akwai lauje cikin nadi - Buba Galadima

Maganar tazarcen da Buhari yake yi akwai lauje cikin nadi - Buba Galadima

- Babban dan hamayya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Alhaji Buba Galadima yayi magana akan maganar tazarcen da shugaban kasar yake yi

- Ya ce duka 'yan jam'iyyar APC ne suke ruruta wuta akan maganar tazarcen saboda shugaban kasar ya samu kofar zarcewa

- Bayan haka kuma ya ce akwai kungiyoyi da ke kiraye-kiraye ga shugaban kasar akan ya nemi cigaba da mulki a karo na uku

Tun a farko dai dama wasu 'yan Najeriya ne karkashin kungiyar dake goyawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya suka bukaci a yiwa kundin tsarin mulkin Najeriya gyara ta yadda shugaban kasar zai samu damar zarcewa a karo na uku.

Duk da dai fadar shugaban kasar ta bakin mai magana da yawun shugaban kasar Garba Shehu ta musanta hakan, inda take cewa shugaban kasar ba shi da ra'ayin tsayawa takara a karo na uku.

Cikakken dan adawar ga shugaban kasar, Buba Galadima ya ce kwata-kwata wannan magana ta fadar shugaban kasa bai aminta da ita ba, inda ya bayyana cewa ba sau daya ba ba sau biyu ba gwamnatin shugaba Buhari ta sha yin amai ta lashe akan wasu abubuwa masu yawan gaske da suka gabata a kasar nan.

Buba Galadima ya kara da cewa idan har hakan ta faru kuwa, kungiyoyin sune na farko da za su zuga 'yan Najeriya cewa ba za ta tafi yadda ya kamata ba matukar ba Buhari ne ya cigaba da mulki ba, inda shi kuma Buhari zai fito daga baya ya ce ai 'yan Najeriya ne suka nemi ya fito ya zarce.

KU KARANTA: Yadda muka yi dambe da wani melamin bogi da yazo cire min Aljanu lokacin ina budurwa - Laila Ali Othman

A yadda Buba Galadima ya ce, gwamnati ba za ta taba fitowa ta musanta wadannan kiraye-kiraye na neman shugaba Buhari ya zarce a kan kujerar mulki karo na uku.

Rahotanni sun bayyana cewa jam'iyyar PDP ce ta fara taso da maganar tazarce a Najeriya inda a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Obasanjo da Goodluck suka yi kokarin zarcewa a kan kujerun mulkin su.

Haka kuma Buba Galadima ya bayyana cewa ya yanke kauna da za a yi zabe na gaskiya a kasar nan, ganin yadda kotu take yanke hukunci kan kararrakin da suka shafi zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel