Boko Haram: Sojoji sun kubutar da mutane 51, sun kama masu alaka da NGOs a Borno

Boko Haram: Sojoji sun kubutar da mutane 51, sun kama masu alaka da NGOs a Borno

Rundunar Sojojin Najeriya ta ce ta inganta atisayen da ta ke gudanarwa a sassa daban-daban na kasar domin tabbatar da cewa 'yan Najeriya sunyi bukukuwan karshen shekara lafiya.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar, Aminu Iliyasu ne ya bayyana hakan ciki wata sanarwar da ua fitar a ranar Laraba a Abuja kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Ya kuma bayyana cewa jami'an sojoji na Sector 3 tare da taimakon sojojin sama na Operation Lafiya Dole sunyi nasarar dakile wani harin da 'yan ta'adda suka kai Gubio a Borno tsakanin ranakun Lahadi da Talata.

A cewarsa, an kashe 'yan ta'adda biyu an kuma kwato babban mota mai dauke da bindiga da bindigu AK 47 guda biyu.

DUBA WANNAN: Zaben gwamnan Kano: An baza 'yan sanda 3,000 yayin da kotu ke shirin yanke hukunci

"Bugu da kari, an ceto farar hula 51 da 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su yayin artabun.

"Dakarun sojojin suna cigaba da mamaye yankin inda suka kai sumame da farmaki.

"Kazalika, sojojin sun kama wasu maza hudu dauke da bushashen kifi mai yawa da za su kaiwa 'yan taddan.

"Ana nan yi musu tambayoyi kuma suna bayar da bayanai masu amfani," inji shi.

Iliyasu ya ce sojojin sun kama wata mota dauke da mata uku da maza 15 da wata shanun sata uku yayin wata sumame da suka kai a karamar hukumar Konduga.

Ya ce an gano cewa wadanda ake zargin ba Shuwa bane kamar yadda su kayi ikirari da farko saboda ba su iya yaren mutanen garin ba.

Iliyasu ya ce binciken da aka fara gudanarwa ya nuna cewa daya daga cikin wadanda ake zargin da wata kungiyar mai zaman kanta da ke tallafawa al'umma (NGOs) a yankin suna musayar bayyanai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel