Wata sabuwa: Bana madigo so suke kawai su bata mini suna - Jaruma Bilkisu Salisu

Wata sabuwa: Bana madigo so suke kawai su bata mini suna - Jaruma Bilkisu Salisu

- Wata sabuwar jaruma ta fito a wani sabon bidiyo ta yi fashin baki akan irin zubar mata da mutunci da ake yi

- Ta bayyana cewa wasu suna amfani da wata lambar waya suna kiran mata da sunanta suna cewa tana so tayi lalata da su

- Ta bayyana cewa ita ba 'yar madigo ba ce kuma ba ta da alaka da wata mace in dai ba mutunci ba

Kamar dai yadda kowa ya sani mutane sun yi kaurin suna wajen yiwa jarumai sharri akan abinda basu ji ba kuma basu gani ba, musamman ma yanzu da aka waye da amfani da kafafen sadarwa na zamani irin su Facebook, Twitter, Instagram da dai sauransu.

A wannan karon ma wata sabuwar jarumar fim ce ta masana'antar Kannywood mai suna Bilkisu Salisu, ta fito a cikin wani sabon bidiyo da ta fitar take kare kanta akan jita-jitar da ake yadawa a kanta na cewa tana yin madigo.

KU KARANTA: Adadin jaruman Kannywood da suka bi doka, da kuma wadanda suka yi tawaye ga hukumar tace fina-finai

Ga abinda sabuwar jarumar take cewa a cikin bidiyon:

"Assalamu Alaikum jama'a sunana Bilkisu Salisu kamar yadda kuka sani, jan hankali ne nake so na yiwa masoyana da 'yan uwana, akwai wata lamba da wata take amfani da shi wacce idan mutum yayi amfani da manhajar True Caller yana fito da sunan Nafisa Abdullahi, ban santa ba kuma bani da alaka da ita, amma tana amfani da sunana tana yiwa mutane magana ta WhatsApp tana cewa ai ni ce tana son su, tana dai maganganu marasa dadi a kaina, ma'ana tana nuna alamun tana son 'yan uwanta mata.

"Jama'a ni ba 'yar madigo ba ce, bana neman mata, bani da wata alaka ta kusa ko kuma ta nesa da mace idan ba mutunci ba, abinda yasa ma na fito nayi magana shine bana so maganar tayi nisa taje wani waje a dinga ganin kamar nice nake yin irin wannan harkar.

"Idan ma wani abu na yiwa wani dan Allah yayi hakuri, bani da wata matsala da kowa, mutunci ne tsakani na da kowa, duk wani wanda muka samu sabani dashi to shine ya jawo, ni bani da matsala da kowa.

"Ko wacece dan girman Allah ta daina yi mini wannan abin da take yi, idan ba haka ba kuma zamu dauki mataki a kai."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel