Kullu Nafsin Za'ikatul Maut: Ladani ya mutu a Masallaci yayin da yake jira lokaci yayi ya kira sallar asuba

Kullu Nafsin Za'ikatul Maut: Ladani ya mutu a Masallaci yayin da yake jira lokaci yayi ya kira sallar asuba

- Daga gareshi muke kuma gareshi zamu koma

- Ladanin Masallacin Al-Sulaimani dake birnin Jiddah ya rasu yayin da yake zaune a cikin Masallacin yake jira lokacin kiran sallar asuba yayi ya kira sallah

Ladanin mai shekara 60 a duniya mai suna Abdul Haq Al Halabi, yana zaune yana karatun Al-Qur'ani sai rai yayi halinsa yayin da ya rage saura mintuna kalilan ya kira sallah.

Ladanin dan asalin kasar Syria ne, kuma yana zaune a kasar Saudiyya kenan sama da shekara 40, kuma an san shi kullum wajen halartar Masallacin, ana kuma ganin shi a lokuta da dama yana karatun Al-Qur'ani mai girma.

An ce kowa zai mutu akan abubuwan da yake yi. Wannan mutuwa da yayi ta zama abin kwatance domin ace ka mutu a cikin Masallaci kuma kana karatun Al-Qur'ani mai girma, yayin da kake jira lokacin sallah yayi ka kira!

KU KARANTA: Yadda fitaccen dan kwallon kafa Sadio Mane ya ginawa Musulmai Makaranta, Masallaci da Asibiti a kasar Senegal

Mu tsaya mu dinga duba rayuwarmu mu dinga tambayar kan mu shin idan mutuwa ta zo zata dauke mu yanzu mun shirya kuwa.

Allah ya jikansa da rahama, ya kyauta makwancinsa, mu kuma idan ta mu ta zo yasa mu cika da kyau da imani. Amin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel