Gwamnatin jihar Neja ta gargadi 'yan Najeriya a kan kalaman nuna kiyayya

Gwamnatin jihar Neja ta gargadi 'yan Najeriya a kan kalaman nuna kiyayya

Sakataren gwamnatin jihar Neja, Alhaji Ibrahim Matane, ya gargadi 'yan Najeriya da su kauracewa zantuttuka na shaci fadi da kalaman nuna kiyayya domin tabbatar da zaman lafiya da kuma aminci a kasar.

Alhaji Matane ya yi wannan kira ne cikin wata sanarwa da sa hannun mai magana da yawaunsa, Lawal Tanko, yayin murnar cikar Najeriya shekaru 59 da samun 'yanci.

Babban jami'in gwamnatin ya nemi 'yan Najeriya da su dabi'antu da soyayyar juna, zaman lafiya, jituwa da kuma girmama junansu ba tare da nuna bambancin ra'ayi na addini, siyasa, ko kuma al'ada ba.

A madadin gwamnan jihar Muhammad Sani Bello, Alhaji Matane ya gargadi al'ummar jihar Neja da su tashi su farga wajen sanya idanun lura domin cin galaba a kan kalubalai da wasu sassan kasar nan ke fuskanta musamman ta'addancin 'yan daban daji, satar shanu, garkuwa da mutane da sauransu.

A rahoton da jaridar BBC Hausa ta ruwaito, tuni dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabinsa ga 'yan kasar da misalin karfe 7:00 na safiyar yau Talata dangane da bikin murnar cikar Najeriya shekaru 59 da samun 'yanci.

KARANTA KUMA: Najeriya tana asarar N5trn a duk shekara ta hanyar satar mai

Shugaban kasa ya yi jawabi mai tsawo cike da bayanai game da manufofi da kuma abin da gwamnatinsa ta APC ta cimma a tsawon shekara hudu na wa'adin farko da ya shafe da kuma abin da za su yi a wa'adi na biyu.

Wani abu da shugaban kasar ya tabo shi ne kalaman nuna kiyayya wanda ya ce za su dauki kwakkwaran mataki a kan duk wanda ya nemi ya matsa wa wani dan kasa, lamarin da ya ce za su sanya kafar wando daya da masu bayyana kalaman batanci da nuna kiyayya.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel