Dole ne gwamnati ta karo hanyoyin hana matasa zaman kashe wando - Rabaran George

Dole ne gwamnati ta karo hanyoyin hana matasa zaman kashe wando - Rabaran George

Rabaran Dealyn George, babban limamin hedikwatar cocin Apostolic Faith dake birnin Abuja, ya shawwarci gwamnatin tarayyar Najeriya da kara samar da hanyoyin hana matasa zaman kashe wando a fadin kasar.

A yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a ranar Lahadi cikin birin Abuja, Georage ya ce za'a samu babban kaso na rangwamin kalubalai da kasar nan ta ke fuskanta matukar an dage wajen samar da aikin yi ga matasa.

Ya ce akwai bukatar gwamnatin ta jibinci lamarin matasa ta hanyar haramta masu zaman kashe wando a kwararo da sakonni na kasar.

Babban limamin ya ce hakan zai tabbata ta fuskar sama wa matasa masu abun dogaro da kai, lamarin da ya ce babu shakka zai taka muhimmiyar rawar gani wajen magance kalubalai da kasar nan take fuskanta musamman rashin tsaro.

KARANTA KUMA: Mayakan Boko Haram sun kashe mutane dama a garuruwan Borno

A wani rahoto da hukumar kididdiga ta Najeriya ta fitar a shekarar 2018 da ta gabata, ta ce yawan marasa aikin yi a kasar ya karu da kimanin kashi 23 cikin 100.

Jaridar BBC Hausa ruwaito cewa, hakan na nuni da cewa 'yan Najeriya marasa aikin yi sun tasar ma miiliyan 20. Hukumar ta bayyana cewa a shekarar bara yawan mutane marasa aikin yi ya karu daga mutane miliyan 17 a shekarar 2017.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel