Na shafe shekaru 13 ina lalata da mijin 'yar uwata kuma har yanzu bata sani - Wata mata ta fadi abinda ke damunta

Na shafe shekaru 13 ina lalata da mijin 'yar uwata kuma har yanzu bata sani - Wata mata ta fadi abinda ke damunta

Wata 'yar Najeriya, da alhaki ya kama, ta bayyana yadda ta shafe tsawon shekaru 13 tana kwanciya da mijin 'yar uwarta tare da neman taimakon jama'a a kan yadda za ta daina aikata wannan cin amana.

Ta bayyana hakan ne a cikin wani da ta aika wa kwararriya a bangaren harkokin masoya da ma'aurata, Cynthia Valerin Raphaels.

"Barka da yau goggo. Na yanke shawarar aiko maki wannan sako ne saboda na kasa samun sukuni a rai na dangane da abinda nake aikata wa. Ina neman shawarar ki, saboda ban san wa zan nufa da wannan labari ba.

"Ba zan damu da irin sukar da masu karanta shafinki zasu yi min ba. Ina zaune tare da 'yar uwa ta a gidan mijinta kimanin shekaru 16 kenan yanzu. Na koma zama tare da 'yar uwa ta ne lokacin ina da shekaru 15 bayan mutuwar iyayenmu. Yanzu kusan shekaru 13 kenan mijinta na kwanciya da ni.

DUBA WANNAN: Ana wata ga wata: Mahaifin da ya daure 'yayansa 2 da sasari na tsawon shekara 2 ya mutu a hannun hukumar NAPTIP

"Ban san ta yaya zan fada wa 'yar uwata cewa na yi mata laifi ba. Yanzu na cika sheakaru 31 kenan amma na kasa daina bawa mijinta hadin kai. Ba fyade yake min ba, kawai yana nuna min kula wa ne, saboda shine ya saka ni a makaranta kuma yake ziyarta ta lokacin da nake karatu a jami'a.

"Ita 'yar uwa ta ma'aikaciyar banki ce, ni kuma yanzu haka ina aiki ne a dakin gwaje-gwaje. Ni ce mai kula da yaran 'yar uwa ta, 'yar uwa ta bata son jin maganar zan bar gidansu wata rana, saboda jin dadin zama da ni da take yi. Ta kan yawan fada min cewa aure ne kawai zai raba ni da gidanta.

"Ki taimaki min 'Madam', bana son cigaba da irin wannan rayuwar amma ban san ta ina zan fara sabuwar rayuwa ba. Ban taba kusantar wani namiji ba bayan mijin 'yar uwa ta. Ina neman shawara, ki taimaka min," a cewar budurwar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel