Tirkashi: Mai gida ya sanya wa matarsa wuta a Ondo

Tirkashi: Mai gida ya sanya wa matarsa wuta a Ondo

Jami’an yan sandan jihar Ondo sun kama wani mutum mai suna Ojo Daniyan, kan zargin aikata kisan kai. An zargi Daniyan da cinna wa matarsa, Dorcas wuta a hanyar Irese, Akure, jihar Ondo, a ranar Asabar, 14 ga watan Satumba, da misalin karfe 11:00 na dare yayinda take bacci.

An tattaro cewa kafin faruwar lamarin, matar da mijinta sun samu sabani kan wani fili da ya siyar.

Wannan ya sanya zargin cewa mijin ne ya aiwatar da ta’asar.

Wata majiya ta bayyana cewa yan sa’o’i kafin lamarin, Daniyan kawo galan din fetur gida; sannan cewa yan sa’o’i bayan nan, Sai wuya ya fara ci yayinda marigayiyar ke cikin dakin.

Kakakin yan sandan jihar, Mista Femi Joseph wanda yayi magana da majiyar mu a ranar Juma’a yace wanda ake zargin na tsare a hannun yan sanda, sannan cewa rundunar ta fara gudanar da bincike cikin lamarin.

KU KARANTA KUMA: Ana can ana bata kashi tsakanin sojoji da 'yan Boko Haram a Borno

A wani labarin kuma mun ji cewa aAn yankewa wata budurwa hukuncin shekara sha uku a gidan yari, bayan an kama ta da laifin yankewa saurayinta mazakuta, saboda ta gano cewa yana nunawa abokanan shi bidiyon yadda suke kwanciya.

Budurwar mai suna Brenda Barattini, mai shekaru 28, ta cirewa saurayin nata mai suna Sergio Fernandez mai shekaru 42 mazakuta shekaru biyu da suka gabata, inda ake tuhumar ta da laifin yunkurin kisa, hakan ya sanya aka yanke mata hukuncin shekaru sha uku a gidan yari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel