Ke duniya: Bidiyon yadda 'yammata masu talla suka je a saka musu robar hana daukar ciki

Ke duniya: Bidiyon yadda 'yammata masu talla suka je a saka musu robar hana daukar ciki

Wani bidiyo da yake yawo ta yawo a kafafen sadarwa ya bayyana yadda wasu 'yammata 'yan talla suka je wani asibiti domin a saka musu wata roba da take hana daukar ciki

Kamar yadda bidiyon ya nuna 'yammatan guda biyu sun shiga har cikin asibitin suka samu ma'aikaciyar asibitin suka bayyana mata abinda ya kawo su babu kunya babu tsoron Allah.

Da matar ta tambayesu dalilin su na yin haka sun bayyana mata cewa talla ce ake kasa musu wacce bata fi ta naira dari biyar ba, amma kuma za a bukaci su kawo kudi sama da haka.

'Yammatan sun bayyana cewa wannan dalilin ne ya sanya suka zo a saka musu wannan roba, sunce duk ranar da basu kai kudin da aka bukaci su kai ba, to ranar ba a basu abinci suci a gida sannan kuma za ayi musu dukan tsiya.

Haka kuma 'yammatan sun roki ma'aikaciyar asibitin da ta taimaka ta sanya musu, inda suka ce ko nawa ne za su biya ta idan har ta amince ta saka musu.

KU KARANTA: An kuma: Wata mata ta sake tona asirin wani dan majalisa da yake lalata da ita

Ma'aikaciyar asibitin ta bayyana cewa ita mata masu aure take sanyawa wannan abin, matan ma sai wadanda mazajensu suka yadda, ko kuma wacce take yawan yin bari, ko wacce ke shan wahala wajen haihuwa.

'Yammatan sun nuna bacin ransu saboda matar ta bayyana musu cewa baza ta saka musu ba, inda har daya a cikinsu take bayyana mata cewa tana da cikin shege.

Matar tayi kokarin ta fadakar dasu akan abinda suke yi sai suka bayyana mata cewa su ba sun zo wajenta domin tayi musu wa'azi bane, idan baza ta saka musu ba ta fada musu.

Ga dai bidiyon yadda abin ya kasance a kasa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel