Ta bar babban tarihi a duniya: Wata mata 'yar shekara 40 ta mutu bayan ta haifi yara 69

Ta bar babban tarihi a duniya: Wata mata 'yar shekara 40 ta mutu bayan ta haifi yara 69

- A kasar Palastine an samu wata mata da ta haifi yara sittin da tara a duniya

- Sai dai kuma matar ta mutu a lokacin da take da shekaru 40 a duniya bayan ta haifi yaran

- An bayyana cewa matar ita ce mace ta farko da ta fi kowacce mace lafiya wajen haihuwa, amma kuma ba ita ce ta farko da ta fara haifar yara masu yawa irin wannan ba

Abin mamaki akwai matar da ta bar tarihi a duniya bayana ta haifi yara sittin da tara. Wannan mata da ta haifi yara sittin da tara dai 'yar asalin kasar Palastine ce. An ruwaito cewa ita ce mace ta farko da ta kowa lafiya a bangaren haihuwa.

A cewar wani gidan talabijin na kasar Saudiyya dake kasar ya bayyana cewa wannan mata dai 'yar kasar Palastine ta mutu bayan ta cika shekara arba'in a duniya. Mijinta shine ya bayyana hakan, inda yace matar tashi ta mutu.

A cewar wani rahoto na Guinness, ya ce matar ba ita ce ta farko da ta fara haifar 'ya'ya masu tarin yawa irin haka ba a wannan lokacin.

KU KARANTA: Babbar magana: Majalisar kasar Iran ta sanya hannu akan wata doka da ta baiwa iyaye maza damar auren 'ya'yansu mata

A shekarun da suka gabata tarihi ya nuna cewa a kasar Russia akwai wata mata mai suna Mrs. Vassilyeva matar wani mutumi mai suna Feodor Vassilyev, ita ma an bayyana cewa ta haifi yara 69 a haihuwa 27 da tayi.

A rahoton da muka samu na wannan mata 'yar kasar Russia ya bayyana cewa ta haifi tagwaye sau goma sha shida (16) wanda suka hada da 'yan hudu guda hudu da kuma 'yan uku guda bakwai.

Likitan da yake duba matar ya bayyana cewa matar ta dauki tazarar shekaru uku ba tare da ta sake haihuwa ba bayan haihuwarta ta farko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel