Wani gari da ake biyan zauna gari banza naira dubu talatin (N30,000) a kowacce rana su dinga kwashe shara

Wani gari da ake biyan zauna gari banza naira dubu talatin (N30,000) a kowacce rana su dinga kwashe shara

- Little Rock City gari ne da yake yankin Arkansas, inda suke da wani tsari na aiki ga zauna gari banza

- Tsarin aikin shine zai dinga biyan zauna gari banzan kudi suna fita suna tsince shara a tituna

- Kowanne mutum zai samu kimanin dala goma, kusan naira dubu uku da dari shida kenan a kudin Najeriya

Idan ana zancen harbo tsuntsu biyu da dutse daya to garin Little Rock yana daya daga cikin garuruwan da suke da aikin yi ga mutane, saboda wani sabon tsari da suka fito dashi wanda zai taimakawa marasa aikin yi su samu abin kashewa sannan kuma garin ya kara samun tsafta.

Wannan sabon tsari da garin ya fito dashi ya fara ne a watan Afrilun shekarar nan, inda shirin yake kokarin ganin ya taimakawa zauna gari banza su dinga samun na kashewa wajen kwashe shara da ake zubarwa a hanya.

KU KARANTA: Labari mai dadi: Shugaba Buhari ya bayyana wani muhimmin aiki da zai samawa matasan kasar nan

Wannan tsari zai saka masu yin wannan aiki su dinga samun kimanin dala goma ($10) a kowaccee awa daya, kusan naira dubu uku da dari shida kenan (N3,600) a kowacce awa daya. Hakan na nufin zasu dinga samun kusan kimanin dala tamanin kenan idan suka yi aiki awa takwas, kusan naira dubu talatin kenan a kowacce rana.

Bayan wannan kudi kuma da suke samu gwamnati ta dauki nauyin duba lafiyarsu, da kuma koya musu sana'o'i da kuma basu gidajen zama na wucin gadi. Hakan yana da nasaba da kokarin da gwamnati take yi na ganin ta kawo karshen masu zaman banza a garin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel