Mabiya darikar Kwankwasiyya sun yi ma Pantami ihun ‘Ba ma yi’, Kwankwaso ya yi shiru

Mabiya darikar Kwankwasiyya sun yi ma Pantami ihun ‘Ba ma yi’, Kwankwaso ya yi shiru

Wani bidiyo da a yanzu haka ya karade kafafen shafukan sadarwar zamani na dauke da yadda wasu daga cikin mabiya darikar siyasar Kwankwasiyya suka ci mutuncin fitaccen Malamin addinin Islama kuma Ministan a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Legit.ng ta ruwaito a cikin wannan bidiyon ana iya ganin Sheikh Isah Ali Pantami, jami’an tsaro da kuma yaran Kwankwasiyya, inda yan Kwankwasiyyan suke yi ma Sheikh Pantami ihun ‘Ba ma yi’, wasu ma suna kokarin cafko shi yayin da jami’an tsaro suka yi ta kokarin kareshi.

KU KARANTA: Buhari ga shuwagabannin duniya: Muna yaki da rashawa ba sani ba sabo

Wannan lamari dai ya faru ne a ranar Talata, 24 ga watan Satumba a filin sauka da tashin jirage na Malam Aminu Kano dake garin Kano a daidai lokacin da Ministan yake kan hanyarsa ta komawa Abuja daga Kano.

Sai dai a daidai wannan lokaci su kuma wasu dalibai 242 da gidauniyar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta dauki nauyin karatunsu sun isa tashar jirgin da nufin tafiya zuwa Legas, inda daga can zasu wuce kasashen Indiya da kuma Sudan.

Sanata Kwankwaso ya dauki nauyin dalibai masu darajar digiri lamba daya ne domin su karo karatun digiri na biyu a fannoni daban daban a jami’o’in kasar Indiya, daga ciki har da jami’ar Sharda, inda dalibai 234 zasu yi karatu a India, 8 kuma zasu yi a Sudan.

Sai dai wannan rashin tarbiyya da mabiyan Kwankwason suka nuna ya janyo cece kuce, inda wasu ke ganin hakan bai kamata ba duba da cewa baya ga kasancewarsa minista, Pantami Malamin addini ne da yake amfanar da al’umma.

Amma su yan Kwankwasiyya suna ganin baya ga cewa Pantami Malami ne, kuma ai dan siyasa ne, don haka duk wanda ya sayi rariya ya san za ta yi zuba, saboda a cewarsu babu dan siyasan da ba’a yi ma ihu.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto babu wani jawabi daga bakin jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso, ko gidauniyarsa ta Kwankwasiyya foundation game da wannan lamari.

Ga bidiyon nan kamar yadda wani ma'abocin shafin Facebook Ibrahim Bello ya daura:

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel