Jami’an hukumar kwastam sun kama dilolin gwanjo 235 a Katsina

Jami’an hukumar kwastam sun kama dilolin gwanjo 235 a Katsina

Jami’an hukumar yaki da fasa kauri watau kwastam sun kama wasu dilolin gwanjo guda 235 daga hannun masu fasa kauri a jahar Katsina, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mataimakin kwanturolan kwastam, Bashir Abubakar ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a garin Katsina a ranar Talata, 24 ga watan Satumba, inda yace a ranar Litinin aka kama kayan a garin Jibia.

KU KARANTA: Gwamnan Borno zai baiwa mutane miliyan 2 marasa aikin yi aiki

A cewar Abubakar da tsakar dare jami’an hukumar suka kai samame wani unguwa dake cikin garin Jibia inda suka kwace kayan, sai dai yace mutanen garin sun kai ma jami’ansu hari sakamakon rashin fahimtar abin da suke je yi.

“A dalilin wannan rikici an kashe mutum daya, yayin da mutane uku suka samu rauni, muna taya al’ummar garin Jibia jimamin wannan abu daya faru.” Inji Bashir.

Bugu da kari, Bashir yace sun kwace kwayoyin kwalin Tramadol guda 20 a iyakokin jahar Katsina, sa’annan ya kara da cewa yan fasa kauri suna amfani da babura wajen safarar shinkafa, kwayoyi da sauran haramtattu kayayyaki.

Bashir yace yan fasa kaurin suna biyan kudi N10,000 zuwa sama ga masu babura don su dinga daukan buhunan shinkafar kasashen waje guda biyar da sauran haramtattun kayayyaki.

Daga karshe, Bashir ya yi kira ga shuwagabannin addini da shuwagabannin al’ummomi da sauran masu ruwa da tsaki dasu dage wajen jan hankulansu yaransu game da illolin fasa kauri.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng